Ganduje ya halarci rantsar da dan majalisar PDP da ya kayar da Jibrin a zaben maye gurbi (Hotuna)

Ganduje ya halarci rantsar da dan majalisar PDP da ya kayar da Jibrin a zaben maye gurbi (Hotuna)

- An rantsar da 'yan majalisar da suka yi nasara a zaben maye gurbi da aka kammala a baya-bayan nan

- Ana zargin Ganduje da raka dan majalisar PDP da ya kayar da dan takarar APC zuwa wurin rantsarwar

- Legit.ng ba za ta iya tantance wannan ikirarin da aka yi ba duba da cewa akwai wani dan majalisar daga Kano da aka rantsar tare da dan majalisar na APC

Ana zargin gwamna Umar Ganduje na jihar Kano da yi wa dan majalisar PDP, Ali Datti Yako da ya kayar da dan takarar APC a zaben maye gurbi na mazabar Kiru/Bebeji a jihar Kano rakiya zuwa Majalisar Tarayya domin rantsarwa.

Yako ya kayar da Abdulmumin Jibrin wanda shine dan takarar jam'iyyar APC ta gwamna Ganduje a zaben maya gurbi da aka gudanar a ranar Asabar 25 ga watan Janairu.

Sabbin 'yan takarar da aka rantsar sun lashe zabukansu ne a jihohin Kano, Cross Rivers, Imo da Bauchi. An kuma rantsar da su ne a ranar Laraba 29 ga watan Janairu.

Wani mai suna D. Olusegun ma'abocin amfani da Twitter wanda shima dan jam'iyyar APC ne kamar yadda shafinsa ya nuna ya yi ikirarin cewa Ganduje ya tafi majalisar ne tare da dan majalisar da "ya maye gurbin Jibrin wurin rantsarwar duk da cewa shi dan jam'iyyar PDP ne."

Olusegun ya wallafa wani hoto da ya yi ikirarin Gwamna Ganduje ne da sabon dan majalisa, Yako a Majalisar Tarayya.

Duk da cewa Legit.ng ba za ta iya tabbatar da ikirarin Olusegun ba, Majalisar Tarayyar a shafin ta na Twitter ta bayyana cewa Ganduje da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun ziyarci majalisar domin rantsarwar.

Alhassan Ado Doguwa, tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, yana daya daga cikin sabbin 'yan majalisar da aka rantsar kuma aka sake zabensa a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Legit.ng ta kuma lura cewa Majalisar Wakilan a sakon da ta wallafa a Twitter ta bayyana Yako a matsayin dan jam'iyyar APC daga Kano. Sai dai ba za a iya tabbatarwa a yanzu ko hakan kuskuren rubutu bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel