Gwamnati ta kama yan N-Power guda 30 da basa aiki, ta sallamesu

Gwamnati ta kama yan N-Power guda 30 da basa aiki, ta sallamesu

Gwamnatin tarayya ta fatattaki wasu mutane 30 masu cin gajiyar tsarin tallafa ma marasa aikin yi da gwamnatin tarayya ta kirkiro na N-Power daga aiki a jahar Adamawa.

Jaridar The Nation ta ruwaito babban jami’a dake sa ido a aikin N-Power a jahar Adamawa, Mary Yuwadi ce ta bayyana haka a ranar Laraba yayin da take ganawa da manema labaru, inda tace ma’aikatan su 30 an sallamesu ne saboda basa zuwa aiki a inda aka tura su.

KU KARANTA: Rai ba a bakin komi ba: Yan fashi da makami sun bindige matashi dan bautan kasa

Mary tace mutanen guda 30 dukkaninsu an daukesu a matsayin malamai ne a karkashin tsarin N-Power domin su dinga karantar da dalibai, amma bincike ya tabbatar da basa zuwa makarantun da aka tura su, don haka aka sallamesu.

“A karkashin tsarin bayar da tallafi na gwamnatin tarayya an dauki matasa 14,100 a jahar Adamawa a fannoni daban daban, don haka gwamnati ta dakatar da albashin wadannan malamai 30, da fatan hakan zai zama izina ga sauran wadanda basa zuwa wurin aikinsu.

“Mun gano cewa wasu daga cikin wadanda suka yi rajista a jahar Adamawa mazauna garuruwan Abuja da Legas ne, amma kuma sun amsan kudaden da ake biyansu, haka zalika muna gano akwai ma’aikatan gwamnati a cikin wadanda suka yi rajista.” Inji ta.

A wani labari kuma, gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana wasu manyan kalubale dake kawo tarnaki, tare da mayar da hannun agogo baya a yakin da Najeriya take yi da kungiyar ta’addanci na Boko Haram fiye da shekaru 10.

Zulum ya bayyana haka a ranar Talata, 28 ga watan Janairu yayin da yake gabatar da kasida a taron kara ma juna sani da kwalejin tsaro ta kasa ta shirya ma dalibanta na kwas 28 a babban birnin tarayya Abuja.

Zulum ya bayyana manyan matsaloli hudu da suka zamto kalubale ga yaki da ta’addanci a yankin Arewa maso gabas da suka hada da; cin hanci da rashawa, tserewar yan gudun hijira daga gidajensu, rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’a da kuma rashin kyakkyawan tsari.

“Kana bukatar abubuwan da suka dace domin kawo karshen yaki, makaman da suka kamata da sauran kayan aiki, amma a yanzu wani babban matsala shi ne rashin aminci tsakanin Sojoji da jama’an gari, wannan babban matsala ne dake damunmu, akwai bukatar shawo kansa.

“Idan har jama’a basu koma garuruwansu ba, yakin ba zai kare ba, saboda akwai bukatar jama’a su koma gidajensu domin cigaba da al’amuransu na yau da kullum.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel