Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Abubuwan da ya kamata ka sani game da sabon Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, Dan Sarkin kano Ado Bayero, dan Sarkin kano Abdullahi Bayero.

Haihuwarsa da Karatunsa

An haifi Alhaji Aminu Ado Bayero ne a shekarar 1961 a unguwar jarkasa dake cikin Birnin Kano.Ya fara karatun sa na Firamare a makarantar kofar kudu a shekarar 1967.

A shekarar 1974, ya tafi kwalegin Gwamnati ta Birnin Kudu domin karatun sakandare. A shekarar 1979, ya Shiga Jami`ar Bayero (B.U.K) ta Kano.

A Shekarar 1987, ya tafi Makarantar koyon tukin jirgin sama ta Oakland California Amurka.

Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi bautar kasa a tashar talabijin ta kasa NTA dake Makurdi, jihar Benue.

Rayuwar aikinsa

A shekarar 1984, ya fara aiki a kamfanin jiragen sama na Kabo da mukamin Jami`in Kula da jama`a. A shekarar 1988, ya koma sashen kula da tafiyar jirgin sama.

A shekarar 1990, lokacin Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya cika Shekara sittin a duniya, sai ya aurawa Alhaji Aminu Ado Bayero `mata biyu kuma ya nada shi Sarautar Dan-majen Kano da aikin hakimci a gundumar Dala.

A watan oktoban 1990, Aminu Ado Bayero ya sami karin girma zuwa Sarautar Danburan Kano.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da mai martana Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero
mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero
Asali: UGC

A shekarar 1992, Mai Martaba Sarkin Kano Ado Bayero ya sake ciyar da Danburan Aminu Ado Bayero zuwa gaba Sarautar Turakin kano daci gaba da Zama na gundumar sa ta Dala.

A shekarar ta 2000, Allah ya yiwa Ciroman Kano, Aminu Sunusi rasuwa, wannan ta bada dama Mai Martaba Sarkin kano Ado Bayero ya ciyar da Sarkin dawakin Tsakar Gida Lamido sunusi Ado Bayero gaba zuwa Sarautar Ciroman kano.

Mako daya da hakan, sai Amrigayi Ado Bayero ya baiwa Turakin kano Alhaji Aminu Ado Bayero sarautar ta Sarkin dawakin Tsakar Gidan kano a shekarar kuma Hakimin Dala.

A Nuwamban shekarar 2014, Sarkin kano Muhammadu Sunusi II ya nadashi a matsayin Wanban Kano kuma Hakimin cikin Birni.

A kwana a tashi Allah ya rubutasa a cikin diwanin sarakunan Fulani ya Zama Sarkin Bichi, ya na da ya daga cikin `ya `yan sarki da Allah ya Albarkace shi da Farin jinin jama`ar kanawa kwarai dagaske.

A yau kuma, 8 ga watan Maris, an nada shi sarkin Kano bayan gwamnatin jihar Kano ta kwancewa Malam Muhammadu Sanusi na biyu rawani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel