Ma'aikatan kamfanonin wutan lantarki sun yi barazanar sake yajin aiki

Ma'aikatan kamfanonin wutan lantarki sun yi barazanar sake yajin aiki

Ma'aikatan kamfanonin wutan lantarki karkashin jagorancin kungiyar ma'aikatan lantarkin Najeriya sun bada wa'adin kwanaki 14 ga gwamnatin tarayya na aiwatar da yarjejeniyar da akayi ranar 11 ga Disamba, 2020.

Sakataren kungiyar, Joe Ajaero, ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba a Legas.

Ajaero ya ce idan har ba'a aiwatar da abubuwan da aka yarje ba cikin kwanaki 14, yan kungiyar zasu koma yajin aikin da suka fara a baya.

Yace: "Mun yi niyyar komawa yajin aiki ranar 27 ga Junairu amma sai muka tuna hakurin da kakakin majalisa da ministan kwadago suka bamu."

"Mun gayyatoku nan ne domin bada wa'adin kwanaki 14 ga gwamnati na ta aiwatar da yarjejeniyar da muka rattaba hannu ranar 11 ga Disamba, 2019."

Bugu da kari, Sakataren kungiyar ya ce zuwa yajin aiki ya zama wajibi saboda irin cin fusktar da karamin ministan Lantarki, ya musu a ganawar da sukayi ranar 27 ga Junairu.

Saboda haka, ya na kira ga ministan ya baiwa kungiyar hakuri.

Ajaero yace abubuwan da suke bukatan gwamnati tayi shine biyan ma'aikatan PHCN 2000 da aka kora fanshonsu.

A baya mun kawo muku rahoton cewa Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kashe kimanin tiriliya biyu cikin shekaru uku da suka gabata domin inganta wutan lantarki a Najeriya, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya laburta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan taron kwamitin tattalin arzikin Najeriya a Abuja.

El-Rufa'i ya ce lamarin wutar lantarkin Najeriya ya gurbace gaba daya kuma gwamnatin Buhari ba zata iya cigaba da kashe kudi haka ba.

Yace: "Gaba daya sashen (wutan lantarki) ya kareraye, yadda aka sayar da kamfanin wutan ni ciwa da dama tuwo a kwarya. Saboda haka akwai matsaloli da yawa."

"Abinda mukayi ittifaki akai shine akwai babban matsala a samar da wutan lantarki......Gwamnatin tarayya ta taimakawa bangaren wutan lantarki da N1.7 Trillion a shekaru uku da suka gabata kuma ba za'a iya cigaba da hakan ba."

Gwamnan ya ce mafitan da ake kokarin samarwa zai batawa wasu rai amma shine hanya daya tilo da za'a iya magance matsalan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel