Neman Buhari ya yi murabus: Fadar shugaban kasa ta mayar wa Sanata Abaribe martani

Neman Buhari ya yi murabus: Fadar shugaban kasa ta mayar wa Sanata Abaribe martani

Mai magana da yawun shugaban kasa Garba Shehu ya yi martani ga Sanata Abaribe da ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya yi murabus daga kujerarsa a matsayin shugaban kasa saboda ikirarin da ya yi na cewa shugaban kasar ya gaza magance kallubalen tsaro da ke adabar kasar.

A martanin da ya yi da shafinsa na Twitter @GarShehu ya ce kiran da Abaribe ya yi na cewa Buhari ya yi murabus 'sakarci ne'.

"Buhari ya yi murabus a kan wane dalili? Kawai domin wasu rukunin mutane suna tunanin ya kamata Shugaba Buhari ya yi murabus, suna tsamanin zai yi murabus din. Wannan kirar na su ba shine ra'ayin 'yan kasa ba.

"Wannan ra'ayin wasu wadanda ke suka daga zaune ido a rufe da suka saba furta maganganu marasa tushe.

"Idan har Shugaba kaman Buhari zai yi murabus, akwai miliyoyin 'yan Najeriya da ya dace suyi murabus ciki har da Sanata Abaribe da ya taimakawa wadanda ake zargi da cin amanar kasa suka gudu.

DUBA WANNAN: Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

"Ya nemi kotu ta bawa Nnamdi Kanu beli, daga lokacin wanda ake zargin ya bace.

"Sanata Abaribe ya ki gabatar da Nnamdi Kanu a kotu a lokuta da dama da aka bukaci hakan amma yana da karfin gwiwar da zai zargi wani da cewa baya biyaya ga doka.

"Kamata ya yi a ce wannan mutumin ya maye gurbin wanda ake zargin da gidan yari.

"Jam'iyyar su Abaribe ta bannatar da dukiyar Najeriya ta bar shi a 2015 yanzu kuma ga shi Shugaba Buhari na kokarin ya gyara abubuwa tun bayan da ya hau kan mulki.

"Buhari yana aiki tukuru don ya tsare 'yan Najeriya daga sharrin 'yan ta'adda da suka fito daga yankin Sahel na Afirka da taimakin 'yan Najeriya da kawayen mu na kasashen waje kuma zai yi nasara. Shi kadai zai iya aiwatar da hakan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel