Himba: Kabilar da mata basa wanka amma da mace ake karrama bako

Himba: Kabilar da mata basa wanka amma da mace ake karrama bako

Kabilar Himba wata kabila ce mai cike da abubuwan mamaki. Ana kiran jama’arta da suna Ovahimba ko Omhimba. Suna rayuwa ne a yankin Kunene da ke kasar Namibia. Idan ana mamakin wannan kabilar, fahimtar al’adarsu kanta abin mamaki ce.

Idan ‘yan kabilar suka yi bako, ana ba bakon mace ya kwanta da ita a matsayin karamci. Suna yi wa jariransu ado da wasu irin duwatsu a matsayin sarka.

Kamar hakan bai isa ba, kabilar nan suna rayuwarsu ne a kebance kuma basu son baki. Suna aiki tukuru don tabbatar da cewa addininsu da al’adunsu basu gurbata ba, don haka ne basu cika son baki ba.

Wannan dalilin ne yasa jama’ar kabilar Himba basu wayewa. Da yawansu suna kiwo ne da noma, yayin da matansu kuwa suka kware wajen yin itace, girki da bai wa mazansu abinci da tsaftataccen ruwan sha.

Himba: Kabilar da mata basa wanka amma da mace ake karrama bako
Himba: Kabilar da mata basa wanka amma da mace ake karrama bako
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kaduna: 'N300 ba zata ciyar dani da 'ya'ya uku ba a rana' - Matar aure ta kai mijinta kara kotun Musulunci

Wasu daga cikin ‘yan kauyen suna da ‘yar wayewarsu da kuma riko da addini. Sun kware a addinan gargajiya. Suna auren mata fiye da daya kuma ana aurar da yara mata da wuri.

Rashin yin wankan jama’ar kabilar nan kuwa shima abin mamaki ne. Kafin mai karatu yayi musu fahimtar da ba dai-dai ba, basu wanka ne saboda yanayin yankin da suke.

Jama’ar kabilar Himba suna rayuwa ne a wata irin Hamada mai tsananin yanayi da rashin ruwa. Wannan ne kuwa yasa basu yin wanka.

Rashin yin wankan kuwa baya sa su muni. Idan mai karatu ya gansu a shigar al’adarsu, abin sha’awa ne ballantana yadda matan ke ado da fatarsu.

Tunda wanka ya zama wani abu daban ga ‘yan kabilar, suna amfani da jar kasa sannan su turara jikinsu wanda hakan ke sa su zauna fes da tsafta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel