Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta bukaci Shugabannin tsaro da su yi murabus

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta bukaci Shugabannin tsaro da su yi murabus

Mambobin majalisar sun yi kira ga shugabannin tsaro da su yi murabus daga kujerunsu. Hakan na daga cikin matsayar yan majalisar bayan sun yi muhawara kan lamarin tsaron kasar a zamansu na ranar Laraba, 28 ga watan Janairu a Abuja.

Wani dan majalisa, Abubakar Fulata, ya sanar da takwarorinsa a zauren majalisar cewa shugabannin tsaron sun yasar da amfaninsu.

A cewarsa, kasar za ta kasance cikin hatsari idan aka bar wadannan mutane suna cigaba da maimaita abu guda tare da sa ran samun banbancin sakamako wajen yaki da matsalolin tsaron da ke addabar kasar.

Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta bukaci Shugabannin tsaro da su yi murabus
Yanzu Yanzu: Majalisar wakilai ta bukaci Shugabannin tsaro da su yi murabus
Asali: UGC

Da yake jagorantar zaman, kakakin Majalisa, Femi Gbajabiamila ya karanto ayar tambayar da Fulata ya dasa ga yan majalisa kan ko shugabannin tsaron su yi murabus daga kujerunsu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Kayi murabus tunda ka gaza samar da tsaro - Shugaban yan PDP a majalisa ga Buhari

Koda dai an samu rabuwar kai a tsakanin yan Majalisar wajen bayar da amsoshinsu, mafi rinjaye na yan majalisar sun amince da hakan sannan aka aiwatar da hukuncin.

A wani lamari makamancin haka, mun ji cewa Wasu sanatoci sun bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sallami shugabannin tsaro na kasar.

Sun kuma yi kira ga murabus din sufeto janar na yansanda, Mohammed Adamu.

Yan majalisar sun gabatar da bukatar ne a gudunmawarsu kan tattaunawa da aka yi game da lamarin tsaro a kasar a lokacin zaman majalisa a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu.

Wadanda suka yi wannan kira sun hada da Shugaban marasa rinjaye a Majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, sanata Musa Sani, Betty Apiafi da Solomon Adeola.

Yayinda sanata Sani ya yi kira ga murabus din Shugaban yan sanda, Apiafi da Adeola sun bukaci shugaban kasar da ya tsige dukkanin shugabannin tsaro.

A cewar yan majalisar, ya kamata a sauya shugabannin tsaron tunda basu da sabbin dabarun yaki da rashin tsaro a kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel