'Yan sanda sun yi wa wata mata zigidir don tabbatar da jinsinta a kasar Kenya

'Yan sanda sun yi wa wata mata zigidir don tabbatar da jinsinta a kasar Kenya

Wata mata yar Kenya wacce Allah ya yiwa baiwar gemu kuma ta kasance kwandastar motar bas a kasar, ta bayyana yadda 'yan sanda suka sa ta yin tsirara haihuwar uwarta a ofishinsu saboda su tabbatar da ko ita mace ce.

Shafin BBC ta ruwaito cewa matar mai suna Theresia Mumbi ta ce 'yan sanda masu bayar da hannu a Nairobi, babbar birnin tarayyar kasar Kenya, sun kama ta, tare da wasu mata sannan suka kai su caji ofis.

Ta ce: "jami'an 'yan sanda su biyu suka same ni, sannan suka bukaci da na tube kayana. Suka duba ni. Ban tabbatar da abinda suka gani ba, sai suka ce in mayar da kayana, in koma bayan kanta. Har yanzu ina tuna kamen da aka yi a watan Yulin 2018 kan bayanan shaida."

'Yan sanda sun yi wa wata mata zigidir don tabbatar da jinsinta a kasar Kenya
'Yan sanda sun yi wa wata mata zigidir don tabbatar da jinsinta a kasar Kenya
Asali: Twitter

Wannan lamari ya sanya Misis Mumbi zama jagorar mata irin ta, masu yanayin halitta kamar na maza, sannan ta ce ta bayar da labarinta domin wayar da kan mata irin ta tare da karfafa masu gwiwa wajen buda murya idan aka muzguna musu.

An samu Mumbi da rashin daidaituwar halitta a jiki, wanda hakan ya sanya gemu ke fito mata.

A matsayinta na matashiya, tana yawan aske gemunta har ya kai ga fatarta na kuraje.

"A shekarun baya, na dakatar da aske gemuna a wani lokaci saboda kurajen da ke fesowa a fatata ya zame mini matsala", cewar ta.

Ta ce da gemun ya girma, sai ta fara ware kanta daga cikin taron mutane, inda ta zabi ta yi sayayyarta da daddare.

Ta kara da cewa shiga wani yanayin rayuwa ya sanya ta zama kwandastar bas, domin samun abun dogaro da kai. inda ta ce a cikin irin yanayi na aikinta, ta kan hadu da mata masu halitta irin nata, inda take basu karfin gwiwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Obaseki ya sha alwashin gasa wa Oshiomhole aya a hannu idan ya cigaba da hargitsa al’amuran APC a Edo

Labarin ya kuma nuna cewa a yanzu haka tana cikin wata kungiya ta mata masu gemu a Kenya, sa'annan a lokacin taronsu, ta kan yi wa matasan mata magana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel