An rantsar da Doguwa a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai

An rantsar da Doguwa a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai

Kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila a ranar Laraba ya rantsar da Hassan Ado Doguwa da wasu sabbin 'yan majalisar wakilai da suka yi nasara a zaben maye gurbi da hukumar INEC ta gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

Kakakin ya kuma sanar da cewa 'yan jam'iyyar APC dungurungun sun amince da zabar Hon. Ado Doguwa a matsayin jagoran majalisa.

Doguwa ya ajiye mukamin ne a watan Nuwamba lokacin da kotun daukaka kara da soke zabensa ta umurci a sake zaben maye gurbi.

Yanzu-yanzu: Gbajabiamila ya rantsar da Doguwa a matsayin jagoran Majalisa
Yanzu-yanzu: Gbajabiamila ya rantsar da Doguwa a matsayin jagoran Majalisa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Wadanda suka hallarci rantsarwar sun hada da gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Sanata Kabiru Gaya, Sanata Barau Jibril, Sanata Ibrahim Shekarau, shugabanin jam'iyyar APC da wasu magoya bayan jam'iyyar da dama.

Tun daga babban kofar shiga majalisa, Doguwa da wasu 'yan majalisa daga Kano da sauran magoya bayansu sun mamaye hanyar shiga majalisar.

Da ya ke sanar da Doguwa a matsayin jagoran majalisa, Gbajabiamila ya ce: "Dukkan 'yan jam'iyyar APC sun amince da mayarwa Hon. Ado Doguwa kujerarsa a matsayin jagoran majalisar wakilai."

'Yan majalisar sun yi maraba da Doguwa cikin farin ciki da murna inda suke ta ambaton 'Jagora, Jagora, Jagora, Jagora kafin a rantsar da shi da bayan rantsarwar.

Bulaliyar majalisar Tahir Mongunu ya gabatar da bukatar Doguwa ya kama aikinsa a matsayin jagoran majalisa inda Hon Taiwo Onanuga ya goyi bayan hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel