N33,000 za a fara biyan masu yi wa kasa hidima - Shugaban NYSC

N33,000 za a fara biyan masu yi wa kasa hidima - Shugaban NYSC

Shugaban hukumar Kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC), Brigediya Janar Shauibu Ibrahim ya ce an kara allawus din da ake biyan masu yi wa kasa hidima zuwa N33,000.

Ibrahim ya bayyana hakan ne yayin da ya ke yi wa 'yan yiwa kasa hidima jawabi yayin ziyarar aiki da ya kai a sakatariyar NYSC a jihar Bauchi.

Ya ce anyi karin ne sakamakon amince da sabon albashi mafi karanci da gwamnatin tarayya ta kaddamar.

A cewar sanarwar da aka fitar a shafin Facebook na hukuma ya ce, "Ibrahim ya ce an yi tanadin biyan sabon albashin a kasafin kudin 2020 kuma za a fara biyan sabon albashin da zarar an kammala tantance kudaden."

DUBA WANNAN: Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

Sanarwar ta ce:"Ibrahim ya yi bayanin cewa sabanin rahotanin da ake yada wa a kafafen sada zumunta, aninihin sabon adadin kudin da za a rika biyan masu yi wa kasa hidima.

"Ya shawarci masu yi wa kasa hidiman su rika lura da tsaron lafiyarsu kuma su guji yada labaran karya a shafukan sada zumunta.

"Ya gargade su da su guji yin tafiye-tafiye ba tare da izini ba kuma idan an basu izinin su guji yin tafiyar dare domin kaucewa miyagu."

A watan Satumba, Ibrahim ya bayar da sanarwar cewa za a kara wa masu yi wa kasa hidima allawus da zarar gwamnatin tarayya ta fara biyan sabon albashi mafi karanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel