Kwallo: Zanga-zangan Magoya Man Utd ta kai har gaban gidan Woodward
Mun samu labari cewa an kai wa daya daga cikin manyan shugaban kungiyar kwallon kafa na Manchester United, Ed Woodward hari a gidansa kwanan nan.
Wasu da ake tunanin Magoya bayan kungiyar Manchester ne sun kai zanga-zangarsu gaban gidan ‘Dan kasuwan da ke Yankin Cheshire a Arewacin Ingila.
A wani bidiyo da ya shiga dandalin sada zumunta, an ga wadannan fusatattun Magoya bayan kungiyar su na jefe-jefe da wake-wake domin yi da Woodward.
Ed Woodward mai shekara 48 ya na da Mace daya ‘Ya ‘ya biyu a Duniya. An yi dace ba ya gida a lokacin da aka yi masa wannan ta’adi a Ranar Talatar nan.
Kungiyar ta fito ta yi jawabi mai kaushi, ta na gargadin duk wanda aka kama da hukunci mai zafi. Za a haramtawa Masu laifin alaka da kungiyar har abada.
KU KARANTA: Saudiyya ta na son sayen kungiyar Newcastle a kan $350m
“Magoya baya su bayyana ra’ayinsu wani abu ne daban, amma kuma a kai ga barnar da zai jefa rayuwar mutane cikin hadari, wani abu ne kuma na daban.”
“Ba za mu dauki wani uzurin yin wannan ba. Mun san cewa Duniya za ta mara mana baya yayin da mu ke aiki da ‘Yan Sanda domin gano wadannan masu laifi.”
Bayan wadannan kalamai da kungiyar Manchester United ta fitar, jama’a da-dama sun fito su na sukar wannan mummunan aiki da ya fito daga Masoyan kungiyar.
Ana zargin Ed Woodward da hana ruwa guda a United ta hanyar kin kashe kudi domin sayawa kungiyar ‘Yan wasa. Yanzu haka Liverpool sun ba ta maki 33.
A wasannin da Man Utd ta buga da Burnley da Tranmere kwanan nan, an ji Magoya bayan kulob din su na sukar Woodward, wanda ya ke rike da lalitar kungiyar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng