Tirkashi: An kusa sanyawa wasu 'yan mata wuta bayan an kama su suna madigo a daki da ranar Allah

Tirkashi: An kusa sanyawa wasu 'yan mata wuta bayan an kama su suna madigo a daki da ranar Allah

- Wasu ‘yan mata biyu masu madigo sun kusa haduwa da ajalinsu bayan da aka kama su suna lalata

- Matasa maza da mata dauke da sanduna, duwatsu da adda ne ke biye dasu bayan anyi musu tsirara da niyyar halakasu

- Wani mutum ne ya samu ya cecesu bayan da ya fito gida ya ga yadda wadannan gungun mutanen ke biye da matan

Wasu ‘yan mata biyu masu madigo sun kusa haduwa da ajalinsu bayan da asirinsu ya tonu suna lalata.

Kamar yadda rahoton Laila News ya bayyana, lamarin ya faru ne a daya daga cikin jihohin yankin Neja Delta. Baya ga taimakon wasu jama’a, da tuni matan sun bakunci lahira don kuwa har anyi musu tsirara.

Mai taimakon ya tambayi matan masu madigo ko sun san dokar abin da suka aikata kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar.

Kamar yadda wanda ya taimakawa matan ya bayyana, “Ina kokarin fita daga gida ne in siyo biredi don karin safe ne na ga anyi wa wasu mata biyu tsirara suna gudu ana bin su. A bayansu kuwa akwai kungiyar matasa mata da maza dauke da sanduna, duwatsu da adduna sune biye da su.

KU KARANTA: Asiri ya tonu: An kama VC na jami'a da ya yiwa daliba cikin shege ya kuma yi mata tsallaken aji

“Yadda ‘yan matan suka cukuikuyeni suna rokon in tseratar dasu ne ya ja hankalina. Daga gani na sai matasan da suke biye dasu suka tsaya suna cewa ‘mai gida ‘yan madigo ne yaran nan’. Da tattausan lafuzza na roki jama’ar nan a kan cewa zan shawo kan lamarin.

“Na kai su dakin shan magani don a duba raunikan da suka samu. Amma kullum akwai tambayar da ke damu na: Me yasa ‘yan Afirka suka dau tsana suka dorawa irin wadannan mutanen? Me yasa suke daukar doka a hannunsu bayan sun san akwai dokar da kundin tsarin mulki ya tanadar wa irin wadannan mutane?”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel