Yanzu-yanzu: An kulle shagon yan kasar China a Abuja kan ha'inci da tsoron Coronavirus (Hotuna)
Hukumar kare kwastamomi da samar da daidaito tsakanin yan kasuwa FCCPC ta kulle babbar shagon Panda Supermarket dake unguwar Jabi, birnin tarayya, Abuja gudun cutar Coronavirus.
Jami'an hukumar sun kai ziyarar bazata shagon bayan samun rahoton cewa suna sayarda jabun kayayyaki kuma sun kebance wani wuri na musamman domin yan kasar Sin.
Bayan gudanar da bincike cikin shagon, an gano daskararrun kayan abincin da aka shigo dasu Najeriya daga kasar Sin ta barauniyar hanya, musamman a irin wannan lokaci da ake tsoron cutar Coronavirus.
Hakazalika an gano kayan suka suka dade da esfiya tun 2013 da kuma wasu masu ranar ranar esfiya da ya saba hankali irinsu 2037, 2089, 2073 da sauran su.

Asali: Facebook

Asali: Twitter

Asali: Facebook
Mun kawo muku rahoton cewa Akalla mutane 56 sun mutu kawo yanzu a sakamakon cutar coronavirus da ta barke a kasar Sin. Wannan cuta ta fito ne a Yankin Wuhan, kafin cutar ta fara zagaya Duniya.
Kawo yanzu akwai mutane 2000 da su ka kamu da wannan cuta a fadin Duniya. Ga jerin kasashe 12 da cutar ta bulla yanzu:
1. Kasar Sin (Daga nan aka gano ta)
2. Australiya
3. Spain
4. Japan
5. Malaysiya
6. Nepal
7. Singapore
8. Faransa
9. Taiwan
10. Koriya ta kudu (South Korea)
11. Amurka
12. Vietnam
13. Dubai
14. Ingila
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng