Bakin kishi: Wata mata ta kone kanta kurmus a jihar Kano

Bakin kishi: Wata mata ta kone kanta kurmus a jihar Kano

- Wata mata mai suna Rabi da ke unguwar Gayawa a karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano ta kashe kanta har lahira

- Ana zargin Rabi ta tattara duk abinda ta ke bukata don kona kanta ne saboda mijinta mai suna Badamasi ya kara aure

- 'Yan uwa da abokan arziki sun bayyana tsananin alhininsu da damuwa sakamakon wannan matakin da marigayiyar ta dauka

Wata mata mai suna Rabi da ke unguwar Gayawa a karamar hukumar Ungogo a Kano ta kona kanta saboda bakin kishi. Matar wacce aka zargi cewa ta tanadi kayayyakin da za ta kona kanta kafin aikata hakan, ta kona kanta ne saboda mijinta mai suna Badamasi ya yi mata kishiya a kwanakin baya, kamar yadda gidan rediyon Freedom Kano ya ruwaito.

A yayin zantawa da wakilin gidan rediyon Freedom da ke Kano, wasu daga cikin ‘yan uwan Rabi sun nuna bakin cikin su a kan aukuwar lamarin.

DUBA WANNAN: Maryam Sanda: Wata matar aure ta sake kashe mijinta a Katsina

Hakazalika, wani dan uwan Badamasi mai suna Salisu Safiyanu ya bayyana yadda lamarin ya auku. Ya ce ya shiga gidan ne amma sai ya ci karo da gawar Rabi a kone, lamarin da ya firgita shi tare da dimauta shi.

Har ila yau, wata shakikiyar kawar Marigayiyar da ake kira da Ramatu, ta nuna tsananin damuwarta a kan matakin da Rabi ta dauka duk da kuwa jami’an tsaro sun hana ganin gawar kawarta.

A lokacin da aka tuntubi jami’an hukumar kashe gobara, kakakin hukumar na reshen jihar kano, Sa’idu Muhammad Ibrahim ya ce yana bin diddigin al’amarin ne.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna kiyawa ya tabbatar da aukuwar lamarin. Ya ce ofishin hukumar kashe gobara sun dau gawar Rabi don mikawa asibiti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel