Tirkashi: Wani ya mutu a cikin akwatin gawa da fasto ya biyashi ya shiga domin su damfari mutane da mu'ujizar karya

Tirkashi: Wani ya mutu a cikin akwatin gawa da fasto ya biyashi ya shiga domin su damfari mutane da mu'ujizar karya

- Wasu majiyoyi da dama sun bayyana yadda wani fasto ya shiga hannun 'yan sanda bayan damfarar da ya shirya ta kwabe

- Ya ba wani mutum dubu dari biyar ne don ya kwanta a akwatin gawa da sunan ya mutu, shi kuwa sai ya tada shi

- Cikin rashin sa'a kuwa, mutumin ya kwanta amma kafin su kai wajen da zai bayyana mu'ujizar sai mutumin ya ce ga garinku

Wasu majiyoyi masu tarin yawa a kafafen sada zumunta sun bayyana yadda wani fasto ya fada halin tsaka mai wuya. Ya biya wani mutum dubu dari biyar don yayi amfani da shi a matsayin 'mu'ujiza' a cikin akwatin gawa don ya damfari jama'a. Amma a rashin sa'a sai mutumin ya mutu.

Wani faston Abuja ya biya wani mutum naira dubu dari biyar don yayi amfani da shi wajen damfara. Mutumin mai sana'ar tireda ya yi karyar ya mutu inda suka shirya cewa faston zai tada shi daga mutuwar.

Tirkashi: Wani ya mutu a cikin akwatin gawa da fasto ya biyashi ya shiga domin su damfari mutane da mu'ujizar karya
Tirkashi: Wani ya mutu a cikin akwatin gawa da fasto ya biyashi ya shiga domin su damfari mutane da mu'ujizar karya
Asali: Facebook

Amma a cikin rashin sa'a, sai mutumin ya mutu a cikin akwatin gawar kafin su kai filin wasan da zasu yi damfarar.

KU KARANTA: Na biya dala biliyan 1 ($1b) domin samar da wutar lantarki a nahiyar Afirka - Mawaki Akon

Matar mutumin ce ta kai kokenta wajen 'yan sanda wadanda suka kama faston bogin kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Amma kuma, an sako faston bayan wasu abokan shi masu kudi a Abuja sun shiga lamarin. Hakazalika, ya ci gaba da damfarar shi a cocin shi da ke Nyanya Abuja.

Sunan faston Bishop Emmanuel Esezobor kuma cocin shi ce Firehouse Church wacce ke kusa da Niger-Delta Gardens and Hotels a Nyanya.

Faston da matar shi a koda yaushe suna samun jama'a da ke tururuwa don zuwa cocin ganin mu'ujizarsu da taimaka musu wajen shawo kan matsalolinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel