Katsina: Mutane sunyi martani kan dokar hana hawa babbur da daddare

Katsina: Mutane sunyi martani kan dokar hana hawa babbur da daddare

Mazauna Katsina sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi a yayin da 'yan sanda suka fara aiwatar da dokar hana amfani da babur daga karfe 7 na dare zuwa 6 na safe a jihar.

Tun a ranar 20 ga watan Janairu ne gwamnatin jihar ta haramta amfani da babura da daddare a jihar. Ta ce an dauki matakin ne domin inganta tsaro a jihar.

Arewa weekly Trust ta ruwaito cewa an fara aiwatar da dokar sosai a cikin birnin Katsina inda masu sana'ar acaba da masu baburan hawa suke dena yawo da zarar lokacin ya yi duk da cewa akwai wasu masu baburan da ke yawo amma ba su hawa manyan tituna duk da cewa jami'an tsaro da suka yi basaja sun kama su.

Wasu mutane a jihar sun fara amfani da keke domin yin zirga-zirga da daddare.

Hana hawa babur da daddare a Katsina: Mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi
Hana hawa babur da daddare a Katsina: Mutane sun bayyana mabanbantan ra'ayoyi
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Kakakin 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya ce an kama masu babbura da dama tun bayan aiwatar da dokar kuma ana gurfanar da su a kotu.

Wasu daga cikin mutane da suka bayyana ra'ayoyinsu sun ce dokar tana janyo musu wahalhalu domin babura suke amfani da shi don zirga-zirga a jihar.

Wani mai sanaar achaba Yusif Mohammed ya ce "Kudin da na ke samu ya ragu sosai saboda galibi da daddare na ke aikin jigilar fasinja da kayayyaki.

"Duk da cewa tsaro ya fi muhimmanci, ya zama dole mu yi hakuri da dokar amma ina fatan ba za ta dade ba za a kyalle mu mu koma aikin mu na dare."

Wani mai sanaar acaba, Abdulkadir ya ce, "Yanzu ma lokacin sanyi ne saboda haka ina maraba da dokar domin babu fasinjoji sosai da daddare."

Sai dai wani mai motan hawa, Halilu Basiru, "ya ce muna maraba da dokar saboda yanzu babu cinkoso a tituna da masu acaba ke janyo wa.

"Yanzu ina jin dadin tuki da daddare, galibi masu sana'ar acaba ne ke janyo mana cinkoso da wasu masu baburan.

"Sun tukin ganganci su na jefa rayuwar sauran masu ababen hawa cikin hatsari amma yanzu an samu sauki."

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa akwai alamun cewa ba za a dage dokar ba da aka kafa bayan Gwamna Aminu Masari ya ziyarci shugaban sojojin saman Najeriya, Air Marsha Abubakar Sadiq kuma ya nemi ya kori masu babura daga cikin daji.

Gwamnan ya ce tun bayan aiwatar da dokan an samu saukin laifuka a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel