Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

Dokar zabe: PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC

Jam'iyyar PDP ta ce ta yi taro da babban wakiliyar Amurka a Najeriya, Ms Claire Pierangelo, a Abeokuta babban birnin jihar Ogun inda ta yi karar abubuwan da gwamnatin jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ke yi.

The Punch ta ruwaito cewa mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa, Yemi Akinhanmi ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ya ke zantawa da manema labarai a Abeokuta.

Ya ce PDP ta yi imanin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba saka hannu kan kudirin yi wa dokar zabe garambawul ba idan ba a tursasa shi ba kuma rashin saka hannu a dokar barazana ce ga demokradiyya.

Shugaban na PDP ya yi ikirarin cewa an gurbata Hukumar zabe mai zaman kanta INEC da bangaren shari'a inda ya kara da cewa ayyukan da gwamnatin APC ke yi na mayar da Najeriya baya.

PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC
PDP ta kai wa gwamnatin Amurka karar APC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Ya ce, "Abinda kawai kawo mafita a kasar shine a tursasa wa shugaban kasa ya rattaba hannu a kan kudirin dokar zabe.

"Kudirin dokar ya kwashe kimanin shekaru hudu a teburin shugaban kasa kuma ya kamata a ratabba hannu a kansa domin demokradiyyar mu ta cigaba a nahiyar Afirka, dole a saka idanu a kai idan ko ba haka ba jikokin mu ba za su san menene demokradiyya ba.

"Mun fada wa wakiliyar Amurka yadda PDP ta inganta demokradiyya a Najeriya cikin shekaru 16. Mun shaida mata yadda gina demokradiyya daga karkara zuwa birane."

Akinhanmi ya ce ya kamata a jinjina wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan saboda dattakun da ya yi na mika wa Buhari mulki ba tare da wani tashin hankali ba.

Pierangelo ta ce an yi taron ne don ganawa da gwamnan jihar kan yadda za a inganta hadin kai tsakanin jihar da Amurka musamman a bangarorin kasuwanci, noma da ilimi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel