Ramuwar gayya: Miji ya harbe matarshi, su kuma matasa sun kone shi kurmus

Ramuwar gayya: Miji ya harbe matarshi, su kuma matasa sun kone shi kurmus

- A safiyar ranar Talata ne yankin Nkporo suka tashi da alhini tare da bakin ciki

- Kanu Ilum ya dau bindiga tare da harbe matar shi wacce ta mutu har lahira

- Fusatattun matasan yankin kuwa suka banka mishi wuta inda ya kone kurmus tare da gidan shi

Da safiyar ranar Talata ne wani mutum a yankin Nkporo a jihar Abia ya harbe matar shi har lahira. Mahaifiyar yara shida: uku maza da uku mata ta rasa ranta ne bayan mai gidanta ya harbeta.

Mutumin mai suna Kalu Ilum, wanda ke a garin mataimakin gwamnan jihar Abia, ya kashe matar shi ne mai suna Chichi da misalin karfe 7 na safiyar ranar Talata.

Ramuwar gayya: Miji ya harbe matarshi, su kuma matasa sun kone shi kurmus
Ramuwar gayya: Miji ya harbe matarshi, su kuma matasa sun kone shi kurmus
Asali: Facebook

Amma kuma sai fusatattun matasan da ke yankin suka banka mishi wuta tare da kone shi da gidan shi kurmus.

KU KARANTA: Zance ya kare: Lauya ta kashe mijinta, ta cire gabansa ta cinye gaba daya

Ya harbi matar shi sau biyu sannan daga baya ya fada rijiya. An yaudare shi don ya fito daga rijiyar amma yana fitowa wasu fusatattun matasa suka banka mishi wuta ya kone.

Ya dade yana barazanar kashe matar ta shi. A lokacin da 'yan uwanta suka nemi sasanta su, an zargi cewa ya bayyana zai harbe ta ya kashe ta kuma babu abinda zai faru. Matar ta so rabuwa da shi amma ya rantse sai ya kasheta idan ta yi hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel