Wata sabuwa: Matan Najeriya sun zo na 15 a jerin matan da suka fi iskanci a duniya a kasashen duniya

Wata sabuwa: Matan Najeriya sun zo na 15 a jerin matan da suka fi iskanci a duniya a kasashen duniya

- Wani sabon rahoto ya bayyana a yanar gizo mai cike da abin mamaki ko kuma al'ajabi

- Rahoton ya bayyana kasashe ne da matansu ke hada abokan jima'i fiye da daya

- Kasar Najeriya ce kuwa ta zo ta 15 a duniya amma kuma ta farko a fadin nahiyar Afirka

Wani sabon rahoto ya bayyana a yanar gizo wanda ya ce matan Najeriya sune kan gaba a nahiyar Afirka wajen hada abokan jima'i masu yawa. A hakan kuma matan Najeriya suka shiga cikin matan kasashe 15 na duniya da ke da wannan dabi'ar, kamar yadda jaridar Information Nigeria ta ruwaito.

A jerin kasashen duniya kuwa, kasar New Zealand ce a kan gaba yayin da Switzerland da Spain suke biye.

Abin mamaki kuwa shine yadda babu kasar Amurka a jerin amma kasashen Slovenia, Italiya, Brazil da Girka ke biye. Kasashen Mexico, Australia da Croatia duk sun samu shiga a sahun gaba.

KU KARANTA: Yara 10 zamu haifa da amaryata - Cewar Sulaiman angon Baturiya

Ga dai jerin kasashe 15 na duniya da matansu ke da abokan jima'i fiye da daya:

1. New Zealand

2. Switzerland

3. Spain

4. Slovenia

5. Italiya

6. Brazil

7. Girka

8. Mexico

9. Australia

10. Croatia

11. The Netherland

12. Jamhuriyar Czech

13. Jamus

14. Faransa

15. Najeriya

Wannan lamarin kuwa ba abin mamaki bane saboda yadda labaran hatgitsi ko kishi tsakanin 'yan mata da samari a Najeriya suka yawaita.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne a jihar Bauchi wani saurayi ya kashe budurwar shi har lahira ta hanyar soka mata wuka a baya.

Kamar yadda majiya mai karfi ta bayyana, saurayin ya dau wannan matakin ne bayan da budurwar ta shi ta amsa wayar wani gardi a gaban shi wajen karfe 1:30 na dare.

Bakin kishi ne ya sarke shi tare da rashin iya sarrafa zuciya. A ranar Asabar kuwa budurwar ta ce ga garinku sakamakon zubar da jini mai tarin yawa da tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel