Kotu ta tausayawa Maina, ta rage kudin belinsa daga N1b zuwa N500m

Kotu ta tausayawa Maina, ta rage kudin belinsa daga N1b zuwa N500m

Babban kotun tarayya dake Abuja a ranar Talata ta rage ka'idojin belin tsohon shugaban kwmaitin gyara harkan fansho, AbdulRashid Maina, daga bilyan daya zuwa milyan dari biyar.

Hakazalika Alkalin ya bukaci Maina ya gabatar da mai tsaya masa guda daya.

A ranar 13 ga Junairu, Maina ya bayyanawa kotu cewa har yanzu ya gaza cika sharruda masu tsaurin gaske da kotun ta kakaba masa na beli a watan Nuwamba.

A ranar Talata, 28 ga Junairu, Alkali mai shari'a, Okon Abang, yace: "Bisa ga hujjojin da aka gabatar gaban kotun, bai kamata in amsa bukatarsa (Maina) ba amma tun ranar da muka dage karar, ya natsu yanzu sabanin yadda yakeyi da farko."

"Zan ji tausayinsa in rage sharrudan."

"Ya biya kudin belin N500 miliyan, ya gabatar da mai tsaya masa kuma wajibi ne ya zama Sanata, wanda zai rika rakoshi kotu kullum."

Alkalin yace wajibi ne Sanatan ya mallaki dukiya a daya daga cikin wadannan unguwannin a birnin tarayya: Kamtape, Central Business District, Wuse 2, Maitama da Asokoro.

Ana zargin AbdulRashida Maina da laifin karkata kudi bilyan 100 na kudin fanshon al'umma.

Kotu ta tausayawa Maina, ta rage kudin belinsa daga N1b zuwa N500m
Maina
Asali: UGC

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta samu umurnina tsare tsohon Shugaban fansho, Mista Abdulrasheed Maina da dansa Faisal, a hannunta har zuwa lokacin da za a kammala binciken da ake cigaba da yi.

An bayar da umurnin ne a ranar 7 ga watan Oktoba, 2019 biyo bayan wani bukata da hukumar yaki da rashawar ta gabatar a kotu, kan ta baiwa hukumar ikon tsare wanda ake karan a hannunta na tsawon kwanaki 14.

Rundunar tsaro na DSS ce ta kama Maina da dansa a wani otel a Abuja biyo bayan taimakon da hukumar ta nema daga wajenta.

Sannan aka mika su ga EFCC domin cigaba da bincike da hukuntasu akan zargin sama da fadi akan wasu kudade.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel