Cin hancin $500,000: 'Zazzabin Lassa ya kashe dan uwan shaidata a Kano' - Farouk Lawan ya fada wa kotu

Cin hancin $500,000: 'Zazzabin Lassa ya kashe dan uwan shaidata a Kano' - Farouk Lawan ya fada wa kotu

Tsohon shugaban kwamitin wucin gadi da majalisar wakilai ta kafa domin binciken biyan tallafin man fetur a 2012, Farouk Lawan, ya sanar da babbar kotun Abuja cewa shaidarsa na farko ya mutu ranar Lahadi bayan kamuwa da zazzabin Lassa a Kano.

Tsohon dan majalisar ya bayyana hakan a gaban kotun yayin zamanta na ranar Talata.

Lawan, ya fadi hakan ne a matsayin hujjarsa ta kin fara kare kansa a tuhumar da aka fara yi masa tun shekarar 2012.

Ana tuhumar Lawan da kabar cin hancin dalar Amurka $500,000 domin cire sunan kamfanin man fetur da iskar Gas mallakar hamshakin dan kasuwa, Mista Femi Otedola.

A ranar 17 ga watan Oktoba na shekarar 2019 ne alkaliyar kotun dake sauraron karar da aka shigar da Lawan tayi watsi da uzurin Lawan na cewa bashi da wani laifi balle ya kare kansa, ya bayyana hakan ne bayan bangaren masu kara sun gabatar da shaidu biyar.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi sabbi nade-nade a CBN, NCC da NCAA

Jastis Angela ta umarci Lawan ya fara shirin kare kansa a tuhumar da ake yi masa, saboda an gabatar da shaidu masu karfi a kan tuhumar da ake yi masa. Kotun ta umarce shi ya fara kare kansa daga ranar 11 ga watan Nuwamba, 2019, amma saboda wasu dalilai da ba a bayyana ba sai kotun ta daga zamanta zuwa ranar Talata, 28 ga watan Janairu, 2020.

Amma, bayan kotun ta zauna a ranar Talata, sai lauyan dake Lawan, Mista Benson Igbanoi, ya sanar da cewa ba zasu iya fara kare kansu ba saboda shaidarsu guda daya "jalli jal" ya rasa dan uwansa, wanda mutu ranar Lahadi a Kano bayan ya kamu da zazzabin Lassa, a saboda haka bai samu damar halartar zaman kotun ba.

Lauyan masu kara ya tabbatar wa da kotun cewa lauyan wanda ake kara ya aika masa da takarda ranar Litinin domin sanar sa shi batun mutuwar dan uwan shaidan.

Alkaliyar kotun ta daga sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel