NEPA 2: Yadda wani matashi ya yi mutuwar ban tausayi a jahar Jigawa

NEPA 2: Yadda wani matashi ya yi mutuwar ban tausayi a jahar Jigawa

Wani matashi mai karambani ya gamu da ajalinsa bayan ya hau saman wata falwayar wutar lantarki ya yi dare dare a karamar hukumar Auyota jahar Jigawa, kamar yadda rundunar Yansandan jahar suka tabbatar.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito cewa sunan matashin da ya rigamu gidan gaskiya Muhammadu Bulala, kuma shekarun 40 a rayuwa, inji mai magana da yawun Yansandan jahar Jigawa.

KU KARANTA: Ba na so a kashe mata ta idan ta kashe ni, a kyaleta ta kula da yaranmu – inji baban soyayya

NEPA 2: Yadda wani matashi ya yi mutuwar ban tausayi a jahar Jigawa
Gwmanan jahar Jigawa
Asali: UGC

Kaakakin Yansandan mai suna Abdu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labaru a ranar Talata, 28 ga watan Janairu, inda yace lamarin ya auku ne a kauyen Gamsarka dake karamar hukumar Auyo da misalin karfe 2:20 na ranar Litinin.

Jinjiri yace Bulala ya hau kan falwayar ne da nufin mayar da wata wayar lantarki da jami’an hukumar rarraba wutar lantarki ta KEDCO suka yanke ta, yana cikin haka ne sai wutar lantarki ta kama shi, kuma nan take ta kashe shi.

“A ranar 27 ga watan Janairu da misalin karfe 3na rana Yansanda sun samu rahoto daga kauyen Gamsarka cewa wani matashi Bulala ya hau saman falwayar wutar lantarki, ya hau da nufin mayar da wata wayar lantarki da KEDCO ta yanke saboda rashin biyan kudin wuta, a sanadiyyar haka wutar ta kama shi, nan take ya fadi ya mutu.” Inji shi.

Jinjiri ya karkare da cewa da fari an mika gawar zuwa asibitin garin Auyo, amma daga bisani aka mika shi ga yan uwansa domin su gudanar da jana’iza a kansa. Amma yace tuni sun fara gudanar da bincike game da lamarin.

A wani labarin kuma, akalla mutane uku ne suka rasa ransu, tare da barnar makudan dukiya a yayin wani kazamar rikicin kabilanci daya barke tsakanin al’ummar Fulani da kabilun Tibabe a kauyen Pangari na karamar hukumar Bali na jahar Taraba.

Wani mazaunin garin mai suna Pius Gura ya bayyana cewa wani bafulatani ne ya shiga gonar wani manomi dan kabilar Tibi mai suna Dooior James, tare da shanunsa, amma a lokacin da manomin ya nemi a biyashi barnar da shanun suka yi masa, sai bahillacen yasa adda ya kashe shi.

Mazaunin garin yana cewa bayan yan uwan manomi Dooir sun samu labarin abin day faru ne sai suka tattara kansu, inda suka kai ma bahillacen harin ramuwar gayya, suka kashe shi, daga nan ne lamari ya ta’azzara.

“Duk a wannan rana (Lahadi), da misalin karfe 6 na yamma ne sai yan uwan bafulatanin suka yi gangami suka kaddamar da farmaki a kauyen manomin, inda suka sake kashe mutum daya, sa’annan suka kona gidaje da dama.” Inji Gura.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel