Ba ni da niyyar ficewa daga PDP in koma APC - Gwamna Ayade

Ba ni da niyyar ficewa daga PDP in koma APC - Gwamna Ayade

- Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River ya kara jaddada cewa ba zai bar PDP ba don komawa APC ba

- A jiya ne gwamnan ya kai wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja

- Wasu daga cikin 'yan majalisar tarayyar jihar sun zargi gwamnan da neman jan su don su sauya shekar tare

Gwamna Ben Ayade na jihar Cross River ya kara jaddada cewa ba zai bar PDP ba don komawa APC ba.

A takardar da mai magana da yawunsa, Christian Ita yasa hannu a ranar Talata, ya ce wannan zargin da ake wa gwamnan bashi da makama balle tushe. Ita, ya ce gwamnan ya je fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan sauyin da masana'antu ke yi ga noma da kiwo a jihar.

"Amfanin ziyarata ga Shugaban Buhari shi ne bayanin halin da jihar ke ciki amma ba siyasar jam'iyya ba. Tattaunawarmu ta shafi halin da asusun jihar ke ciki da kuma yadda jihar ta rasa Bakassi a kotun koli," Ayade ya ce.

Ba ni da niyyar ficewa daga PDP in koma APC - Gwamna Ayade
Ba ni da niyyar ficewa daga PDP in koma APC - Gwamna Ayade
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Wakilin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, wasu 'yan majalisar tarayya na jihar karkashin jam'iyyar PDP sun zargi gwamnan da bayyana kudirinsa na komawa jam'iyyar APC.

A yayin zantawa da manema labarai a garin Calabar, 'yan majalisar da suka bukaci a boye sunansu sun zargi gwamnan da yunkurin kakaba musu 'yan takara a zaben kananan hukumomin jihar da na jam'iyya da ke karatowa.

"Wannan shiryayyen tsari ne. Idan 'yan takararsa suka tsaya a APC kuma suka ci, shima sai ya sauya sheka ya koma tare dasu. Gwamnan ya gana da shugaban kasa jiya kuma hakan ya jawo tashin-tashina a jam'iyyar. Yayi kokarin jan wasu 'yan majalisar don mu canza sheka tare da shi amma mun ki." Mai magana da yawun 'yan majalisar ya sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel