Dungurungum: Kakaki, shugaban masu rinjaye da mambobi 6 na majalisar Imo sun koma APC

Dungurungum: Kakaki, shugaban masu rinjaye da mambobi 6 na majalisar Imo sun koma APC

- Kakakin majalisar jihar Imo ya canza sheka zuwa jam'iyyar APC tare da wasu 'yan majalisa 7

- Ga masana siyasa, sun ce hakan ya biyo bayan hukuncin kotun koli ne da ta kwace kujerar Emeka Ihedioha tare da maye gurbinsa da dan APC

- Bayan sanar da sauya shekar, an dage ci gaba da zaman majalisar zuwa ranar Alhamis mai zuwa

Kakakin Majalisar jihar Imo, Chiji Collins ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya sauya sheka zuwa All Progressives Congress (APC).

'Yan majalisar sun sanar da ficewarsau daga jam'iyyar ne bayan majalisar ta dawo hutu na mako daya da suka tafi.

Kakakin majalisar ne ke wakiltar mazabar Isiala Mbano karkashin jam’iyyar APGA wacce ya bari ya koma ja’iyyar PDP, sannan ya samu kujerar kakakin majalisar bayan an ware ta ga mazabar Okigwe, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sauya shekarsa kamar yadda masu lura da siyasa suka sanar, sun ce yayi hakan ne sakamakon hukuncin kotun koli wanda ya sauke Emeka Ihedioha na jam’iyyar PDP kuma ya maye gurbinsa da Hope Uzodinma na jam’iyyar APC.

Kakakin majalisar ya sanar da canza shekarsa da ta wasu ‘yan majalisar guda bakwai a taron majalisar da aka yi a ranar Talata.

Dungurungum: Kakaki, shugaban masu rinjaye da mambobi 6 na majalisar Imo sun koma APC
Dungurungum: Kakaki, shugaban masu rinjaye da mambobi 6 na majalisar Imo sun koma APC
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

An dage cigaba da zaman majalisar ne wanda dama minti 15 ya dauka bayan da kakakin majalisar ya sanar da sauya shekarsa.

Wadanda suka sauya shekar tare da kakakin sun hada da: Dominic Ezerioha mai wakiltar Oru ta yamma, Chigozie Nwaneri mai wakiltar Oru ta gabas, Kanayo Onyemaechi mai wakiltar Owerri ta yamma, Kennedy Ibe mai wakiltar Obowo da Onyemaechi Njoku mai wakiltar Ihitte/Uboma.

Eddy Obinna mai wakiltar Aboh Mbaise ya koma APC duk da kuwa karamar hukumarsu daya da Emeka Ihedioha.

Da wannan sauya shekar da ‘yan majalisar suka yi, kashi biyu bisa uku na ‘yan majalisar ‘yan jam’iyyar APC ne don haka su ke da rinjaye a majalisar.

Bayan sanar da sauyin shekar, an dage ci gaba da zaman majalisar har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel