Gidan yari ne ya dace da matan da ke hana mazansu kwanciya dasu - Mzee Jackson Kibor

Gidan yari ne ya dace da matan da ke hana mazansu kwanciya dasu - Mzee Jackson Kibor

- Mzee Jackson Kibor sananne ne a kasar Kenya wanda ya saba hawa kanun labarai a kan matsalolin saki da auratayya

- Kibor ya bukaci gwamnati da ta fara daure mata masu hana mazansu kwanciyar aure da su na shekaru biyu a gidan yari

- Ya ce namiji na biyan sadaki ne don duk lokacin da ya so ya samu natsuwa, hana shi dai-dai yake da fashi babu makami kuma da rana tsaka

Mzee Kibor yana shiga kanun labarai ne a lokuta daban-daban a kan matsalolin da suka shafi sakin aure. Sau da yawa matsalar shi ita ce matan shi na hana shi kwanciya da su wanda ya ce hakkin shi ne yake bukata.

Kamar yadda ya bayyana, duk matan da suke hana mijinsu kansu to kamata yayi ya a kama su da laifin cin zarafi kuma a garkamesu a gidan yari na tsawon shekaru biyu don hakan ya zama jan kunne ga mata.

Gidan yari ne ya dace da matan da ke hana mazansu kwanciya dasu - Mzee Jackson Kibor
Gidan yari ne ya dace da matan da ke hana mazansu kwanciya dasu - Mzee Jackson Kibor
Asali: Twitter

Mutumin dan asalin kasar Kenya ya bayyana cewa ana ba maza kunya tare da nuna su matukar aka gane suna cin zarafin matansu, me zai sa kuwa a kyale mata masu wulakanta mazansu tare da hana su abinda halal din su ne?

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Saurayi yayi kokarin yankewa mahaifiyarsa gaba, saboda taje tana zina da wasu a titi

Mzee Kibor yayi wannan maganar ne a wani tattaunawar gidan rediyo da aka gayyace shi.

Maina daya daga cikin wadanda aka gayyata kuma mai kare mata ta ce hakan bai dace ba don sanin mata da aka yi da rauni.

Kamar yadda ya ce, "Namiji ne ke biyan sadaki don ya samu wajen da zai dinga hutawa na halas, amma sai a samu matar ta hana shi hakkinshi, wannan kuwa dole ne a kira shi da fashi babu makami amma da rana tsaka."

Ya kara da cewa, idan aka tabbatar da dokar, toh ya kamata a ce har da maza masu hana matansu hakkokinsu ya kamata a dinga daurewa a gidan yari. Don kowanne daga cikinsu na da hakki a kan daya wanda ya rataya kuma tilas ne a sauke shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel