Yammata sun hadu sun yiwa wata budurwa dukan kawo wuka saboda ta nemi kwacewa daya daga cikinsu saurayi

Yammata sun hadu sun yiwa wata budurwa dukan kawo wuka saboda ta nemi kwacewa daya daga cikinsu saurayi

- Bidiyon wata mata na shan jibga hannun wasu 'yan mata ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani

- Daya daga cikin 'yan matan masu dukan ta bayyana cewa sun zargi matar ne da yunkurin kwanciya da saurayin da ba nata ba

- 'Yan matan da aka dinga hasashen daliban jami'ar Ambrose Ali ne sun yaudari matar ne ta je wajen a kan cewa zasu bata dubu dari

Bidiyon wata mata da aka ga wasu 'yan mata sun yi mata tsirara kuma suna dukanta ya yawaita a yanar gizo kuma ya jawo cece-kuce. Sun zargeta ne da yunkurin kwanciya da wani mutum wanda ba saurayinta bane.

Kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito, daya daga cikin 'yan matan ta ce sun yaudari budurwar ne har ta zo wajen ta hanyar yi mata alkawarin naira dubu dari. Wata daga cikin 'yan matan kuwa an ji tana cewa "kina son lalata min dangantaka ta da shi bayan muna gab da yin aure".

DUBA WANNAN: Tashin hankali: Saurayi yayi kokarin yankewa mahaifiyarsa gaba, saboda taje tana zina da wasu a titi

Ita kuwa wacce aka kama din ta gurfana tana rokonsu yayin da suke dukanta tare da fizgar gashin kanta yayin da suke bidiyon.

Har yanzu dai ba a tabbatar da inda lamarin ya faru ba amma masu hasashe a yanar gizo sun ce daliban jami'ar Ambrose Ali ne da ke Ekpoma, jihar Edo. Wasu kuwa cewa suka yi 'yan matan garin Warri ne da ke jihar Delta.

Yammata sun hadu sun yiwa wata budurwa dukan kawo wuka saboda ta nemi kwacewa daya daga cikinsu saurayi
Yammata sun hadu sun yiwa wata budurwa dukan kawo wuka saboda ta nemi kwacewa daya daga cikinsu saurayi
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel