Asirin wani likitan bogi ya tonu a Kano

Asirin wani likitan bogi ya tonu a Kano

Bayan ya kwashe shekaru masu yawa yana aiki a matsayin likita, wani mutum da aka bayyana cewa likitan bogi ne ya shiga hannun hukuma a jihar Kano.

Hukumar kula da lafiya na jihar Kano (PHIMA) da ke karkashin ma'aikatan lafiya ta kasa tare da hadin gwiwar kungiyar likitocin Najeriya NMA ne suka kai wata sumame kuma suka kama mutumin mai suna Ibrahim Adamu.

Adamu ya dade yana ikirarin cewa shi kwararren likita ne mai lasisin aiki kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Da ya ke magana da manema labarai jim kadan bayan kamen, sakataren PHIMA, Dakta Usma Tijjani Aliyu ya ce sun dade suna bibiyan wanda ake zargin.

Asirin wani likitan bogi ya tonu a Kano
Asirin wani likitan bogi ya tonu a Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan unguwa sun kona wani mutum da ya bindige matarsa da ta siya masa gida da mota

Ya ce an kama Adamu ne bayan sun samun rahoton cewa yana yawo a asibitocin jihar har ma da asibitocin jihohin da ke makwabtaka da Kano.

Dakta Usman ya ce wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda suna cigaba da bincike a halin yanzu.

Ya ce wanda ake zargin ya tabbatar da zargin da ake masa inda ya ce yana aiki ne da takardun wani likitan da ya sace ba tare da saninsa ba.

A wani rahoton, kunji cewa rundunar 'yan sandan jihar kano ta ce ta cafke wasu mutane uku da atke zargi da siyen kuri'a da kudi a yayin zaben maye gurbi a jihar na ranar 25 Janairu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Abdullahi Haruna, ya tabbatar da akamen a takardar da ya fitar a ranar talata a jihar Kano. An yi zaben maye gurbin majalisar wakilan tarayya da na majalisar jihar ne a kananan hukumomi tara na jihar.

Kujerun majalisun tarayyar da zaben maye gurbin ya shafa sun hada da Kiru/Bebeji, Tudun Wada. Doguwa da Kumbotso. Na majalisun jiha sun hada da Madobi, Minjibir, Rogo da Bunkure.

An yi zaben cikin zamn lafiya da lumana a yankunan da zaben ya shafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel