Yan siyasan Najeriya za su samu karin albashi – Hukumar rarraba kudaden gwamnati

Yan siyasan Najeriya za su samu karin albashi – Hukumar rarraba kudaden gwamnati

Hukumar tattarawa tare da rarraba kudaden gwamnatin tarayya, RMAFC ta bayyana cewa ta fara aikin dubawa tare da gudanar da nazari a kan albashin duk wasu masu rike da mukaman siyasa a Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban hukumar RMAFC, Elias Mbam ne ya bayyana haka inda yace akwai yiwuwar albashin yan siyasa da masu rike da mukaman siyasa zai karu matuka bayan sun kammala gudanar da nazari a kan kudaden da suke samu.

KU KARANTA: Tsohon shugaban kasa IBB na nan da ransa, Inji hadimansa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mbam yace zasu tabbata karin albashin ya yi daidai da halin da ake ciki, duk kuwa da cewa gwamnatin kasar na kuka kan rashin samin isassun kudaden shiga, kuma masana sun koka bisa irin bashin da gwamnati ke ciyowa.

“Za mu gudanar da nazari game da albashin masu rike da mukaman siyasa a wannan shekarar, kuma aikin zai tabbatar da ko albashin yan siyasan zai ragu ko kuwa zai karu, wannan na daga cikin ayyukan da zamu gudanar don tabbatar da albashinsu ya yi daidai da halin da ake ciki.” Inji shi.

A yanzu haka shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari na daukan albashin daya kai naira miliyan 3.5 a shekara, yayin da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo yake amsan naira miliyan 3.03, kamar yadda RMAFC ta bayyana.

Minista a Najeriya yana daukan albashin naira miliyan 2.02 a shekara, karamin minista N1.95m, babban mashawarcin shugaban kasa N1.95m, gwamnoni naira miliyan 2.22, mataimakin gwamna naira miliyan 2.11 yayin da kwamishina ke daukan naira miliyan 1.33 a shekara.

Sai dai ba’a nan gizon ke sakar ba, saboda akwai alawus alawus da dama da doka ta amince a baiwa yan siyasa, inda shuagban kasa ke samun alawus na ‘wahala’ kashi 50 na albashinsa, alawus na ‘aiki kullum’ kashi 250 na albashinsa, alawus na mota kashi 400 na albashinsa da sauransu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel