A sauya wa Amotekun suna, daga bible aka samo sunan: Kungiyar musulmi ta yi korafi

A sauya wa Amotekun suna, daga bible aka samo sunan: Kungiyar musulmi ta yi korafi

Kungiyar musulunci ta Muslim Rights Concern (MURIC) ta bukaci gwamnonin jihohin Kudu maso yamma su yi wa hukumar tsaro ta Amotekun garambawul.

Hukumar tsaron da aka yi wa lakabi da Amotekun na nufin Damisa a harshen Yarabanci.

A cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin, shugaban MURIC, Ishaq Akintola ya ce asalin karmar Amotekun daga Bible ya samo asali saboda haka ba zai yiwu musulmi su iya shiga rundunar ba.

Ya ce, "Jeremiah surah ta 5:6 ta ce, "Damisa ne zai tsare birnin su'. An ambaci Amotekun a wannan ayar da ke da alaka da tsare gari. A yanzu, muna da yanki da ke fuskantar kallubalen tsaro na shekaru yanzu kuma sai aka bullo da rundunar tsaro mai sunan Damisa da ake ambaci cewa za ta tsare gari a bible."

"Wannan da gangan aka yi. Wadanda ke kula da harkokin Amotekun da gangan suka ciro sunan daga bible don su danganta abin da addini. Wannan abu ne mai muhimmanci a wurin mu. Don mene za a bawa hukumar tsaro suna mai alaka da addini?

'Asalin Amotekun daga Bible ne' - MURIC ta nemi a yi wa rundunar tsaron garambawul
'Asalin Amotekun daga Bible ne' - MURIC ta nemi a yi wa rundunar tsaron garambawul
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki

"Muna bawa masu tsara wannan sabon hukumar tsaron su sauya mata suna domin tabbatar da zaman lafiya a yankin. Dole ayi hakan idan ana son dukkan masu ruwa da tsaki su bada hadin kai. Kalmar Amoketun za ta janyo rikici. Ba mu bukatar hukuma ta kirista kuma ba mu bukatar ta musulmi. Kamata ya yi hukumar tsaron na Kudu maso yamma ta kasance ta kowa ba wai wani addini ba.

"Mun san cewa musulmi ke da rinjaye a yankin kudu maso yamma saboda haka ba zai yiwu a kafa wata hukuma na hadin kan Yarabawa ba ba tare da saka musulmin yankin a ciki ba. Mu mutane ne masu kulawa da tsaro.

"Za mu shiga hukumar tsaro ta Kudu maso yamma idan ba gwamutsa shi da kiristanci ba. Za mu samu natsuwa idan akwai shugabanin musulmi a ciki ba wai fastoci da bishop da archbishops kadai ba.

"Ya kamata a lura cewa hukumar tsaro da ta fara yi wa 'yan uwan mu musulmi na wani yankin barazana ba alheri bane gare mu a kasar Yarabawa. Babu kabilanci ko nuna banbancin launin fata a musulunci (Kurani 49:13). Musulmi 'yan uwan juna ne. Musulmi Yarabawa suna son garinsu. Amma kuma Allah ya ce su so 'yan uwansu mata da maza ba tare da banbancin launin fata ko kabila ba."

A baya, Akintola ya zargi gwamnonin Kudu maso yamma da daukan zalla aiki a hukumar ta Amoketun da ya kira yan bindiga.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel