Yadda na tsallake rijiya da baya yayin da 'yan bindiga suka kai hari gona ta - Gwamna Ortom
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Litinin ya ce wasu 'yan bindiga da ake zargi makiyaya ne sun kai masa hari a gonarsa da ke Makurdi-Naka a Makurdi, babban birnin jihar a makon da ya gabata.
The Cable ta ruwaito cewa Ortom ya fadi hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai a Makurdi, inda ya ce hakan ba zai sa ya firgita ya dena magana don kare mutanensa ba.
Ya kuma sake jadada kirarsa ne neman a kama shugabanin kungiyar Miyetti Allah kan zarginsu da neman tayar da fitina a jihar.
Ortom ya ce, "Na tafi gona ta a makon da ya gabata kuma wasu makiyaya masu yawa da ke hanyarsu da koma wa Benue sun bude min wuta."

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Abin kunya: Siriki ya dirkawa amaryar mahaifin matarsa ciki
Ya ce dakarun sojoji na Operation Whirl stroke da hedkwatan tsaro na kasa suka kafa ne suka cece shi.
Ortom ya bayyana damuwarsa kan yadda ake bari makiyaya su rika yawo da makamai na zamani da suka fi na jami'an tsaro amma ana kama manoma idan an same su da adda
Ya ce makiyayan ba suna zuwa jiharsa bane don yin kiwo sai dai kawai domin su haddasa fitina.
Ortom ya ce yanzu Najeriya ba kaman zamanin baya bane a shekarun 50s da 60s da makiyaya ke yin kiwo kyauta.
Ya ce, "Har yanzu dokar hana kiwo a fili na jihar tana nan tana aiki saboda haka duk wanda ya ke son yin sana'ar kiwo ya zama dole ya rungumi tsarin killace dabobi a wuri guda."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng