KAROTA zata fara kwacen adaidaita marasa rijista a Kano

KAROTA zata fara kwacen adaidaita marasa rijista a Kano

KAROTA a jihar Kano za ta fara kwace ababen hawa marasa rijista a jihar daga ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu.

Manajan daraktan KAROTA, Alhaji Baffa Dan agundi ya sanar da hakan a ranar Litinin tare da tabbatar da cewa za a rufe yi wa adaidaita sahu rijista a jihar a daren Laraba.

Kamar yadda takardar da kakakin cibiyar, Nabilusi Abubakar Kofar Na'isa ya fitar kuma jaridar Solacebase ta samu, ta ce an yanke wannan shawarar ne a ranar Litinin bayan taron da shugabannin kungiyoyin 'yan adaidaita suka yi a jihar.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa dukkan rijistar dai ta kama dubu ashirin hudu ne na kowanne adaidaita.

DUBA WANNAN: Hukuncin kisa: Muhimman abubuwa a kan alkalin da ya yanke wa Maryam Sanda hukunci

Takardar ta ce, Baffa Dan Agundi ya ja kunne a kan cewa hukumar ba za ta sassautawa duk wanda ta kama babu takardun rijista ba a jihar tunda dai ta bada lokacin yin rijistar.

"Duk wanda aka kama ba tare da lasisin aiki ba za a kama shi ne a matsayin mai laifi da ke niyyar samar da matsala a jihar," takardar ta ce.

Kamar yadda manajan daraktan ya sanar a takardar, duk wanda ya karya dokar kuwa za a kwace adaidaita sahun na shi dugurungun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel