Gwamnoni 7, manyan sarakuna, da jiga-jigan da suka halarci bikin rantsar da Yahaya Bello

Gwamnoni 7, manyan sarakuna, da jiga-jigan da suka halarci bikin rantsar da Yahaya Bello

Akalla gwamnoni 7 na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) suka dira Lokoja ranar Litinin domin halartan bikin rantsar da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, karo na biyu.

An gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar dake Lokoja.

Ga jerin gwamnoni, sarakuna da yan siyasan da suka halarta:

1. Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi na jihar Ekiti Chairman APC Governors Forum, Governor

2. Shugaban kungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagaudu na jihar Kebbi

3. Simon Lalong na jihar Plateau

4. Abdulrasak Abdulrahman na jihar Kwara

5. Rotimi Akeredolu na jihar Ondo

6. Maimala Buni na jihar Yobe

7. Babagana Zulum na jihar Borno

8. Shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomole,

9 Sanata Smart Adeyemi,

10 Sanata Jibrin Isah,

11. Sanata Oseni Yakubu

12. Atta Igala, HRH Michael Amen Oboni,

13. Ohinoyi of Ebiraland, Alhaji Ado Ibrahim,

14. Obaro of Kabba, Oba Solomon Owoniyi,

15. Ohimege Igu of Koto Karfe, Alhaji Abdulrasak Isah Koto.

An rantsar da Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a ranar Litinin, 27 ga watan Janairu domin sake shugabancin jihar a karo na biyu a Lokoja, babbar birnin jihar.

Shugaban alkalan jihar ne ya rantsar da Bello tare da abokin takararsa a zaben watan Nuwamba, Edward Onoja, Channels TV ta ruwaito.

Taron ya samu halarta wasu gwamnoni da manyan jami’an gwamnati a sauran masu fada a ji.

Hukumar INEC ce ta kaddamar da Yahaya Bello dan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashezaben gwamnan jihar Kogi.

Hukumar zaben ta bayyana cewa Bello na APC ya samu kuri’u mafi yawa a zaben wato guda 406,222 inda ya kayar da Musa Wada na PDP wanda ya samu kuri’u 189,704 a zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel