Allah kare: Zazzabin beraye ‘Lassa’ ya halaka mutane 4 a jahar Taraba

Allah kare: Zazzabin beraye ‘Lassa’ ya halaka mutane 4 a jahar Taraba

Cutar zazzabin beraye, watau Lassa Fever ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu a jahar Taraba tun bayan barkewar cutar a jahar, kamar yadda kwamishinan kiwon lafiya na jahar, Innocent Vakkai ya tabbatar.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin 27 ga watan Janairu a garin Jalingo, babban birnin jahar Taraba, inda yace an samu bullar cutar a wurare 15 a jahar, amma mutane 4 ne kawai aka tabbatar da kamuwarsu, yayin da 5 suka mutu.

KU KARANTA:

Kwamishina Vakkai ya bayyana kananan hukumomin jahar guda 6 da aka samu bullar cutar kamar haka; Bali, Gashaka, Gassola, Ardo-Kala, Jalingo da kuma Ibbi. Sai dai kwamishinan yace sun samar da wani tsari don kula da cutar tare da gano duk inda ta bulla da kuma yadda za’a kiyaye wanzuwarta.

Haka zalika kwamishinan yace gwamnatin na kokarin wayar da kawunan jama’an jahar game da alamomin cutar Lassa Fever, sai dai ya bayyana kalubalen da suke fuskanta game da cutar da suka hada da tsaikon da ake samu na kai rahoto ga asibibitoci saboda matattun hanyoyin jahar.

Daga karshe kwamishinan yace ma’aikatar gwamnatin tarayya za ta samar ma gwamnatin jahar na’u’rorin gudanar da gwaje gwaje a kan cutar zazzabin Lassa, haka nan gwamnatin jahar na shirin sayo na’urar da kanta don gudun bata lokaci.

A wani labari kuma, akalla mutane uku ne suka rasa ransu, tare da barnar makudan dukiya a yayin wani kazamar rikicin kabilanci daya barke tsakanin al’ummar Fulani da kabilun Tibabe a kauyen Pangari na karamar hukumar Bali na jahar Taraba.

Wani mazaunin garin mai suna Pius Gura ya bayyana cewa wani bafulatani ne ya shiga gonar wani manomi dan kabilar Tibi mai suna Dooior James, tare da shanunsa, amma a lokacin da manomin ya nemi a biyashi barnar da shanun suka yi masa, sai bahillacen yasa adda ya kashe shi.

Mazaunin garin yace bayan yan uwan manomi Dooir sun samu labarin abin day faru ne sai suka tattara kansu, inda suka kai ma bahillacen harin ramuwar gayya, suka kashe shi, daga nan ne lamari ya ta’azzara.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel