Mahara yan bindiga sun bude ma jama’a wuta a Filato, dayawa sun mutu
Wasu gungun miyagu yan bindiga sun kai mummunan farmaki a unguwar Kwatas na karamar hukumar Bokkos na jahar Filato inda mutane da dama suka mutu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan jahar Filato, Simon Bako Lalong ya tabbatar da harin, inda ya bayyana shi a matsayin wani yunkuri da makiyan jahar ke yi don ganin sun mayar da lalata zaman lafiyar da aka samu a jahar, tare da mayar da hannun agogo baya.
KU KARANTA: Boko Haram: Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 3 a Masallaci a Borno
Gwamna Lalong ya jajanta ma mutanen da harin ya shafa, sa’annan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk inda yan bindigan suka shiga da nufin gurfanar dasu gaban kotu domin su fuskanci hukuncin abin da suka aikata.
Wannan hari dai ya faru ne bayan kimanin makonni uku da aka samu kwatankwacinsa a kauyen Kunben na karamar hukumar Mangu inda mutane 12 suka mutu, kuma kimanin mako 1 kenan da wasu yan bindiga suka sace shanu 73, da tumani 23 daga garken wasu Fulani a kauyen Bisichi na garin Barikin Ladi.
A nata jawabin, rundunar Yansandan jahar Filato ta bakin mai magana da yawunta, ASP Ubah Gabriel Ogaba ta bayyana cewa a yanzu haka Yansanda sun nufi inda aka kai harin domin tabbatar da halin da ake ciki.
A wani labari kuma, akalla mutane uku ne suka rasa ransu, tare da barnar makudan dukiya a yayin wani kazamar rikicin kabilanci daya barke tsakanin al’ummar Fulani da kabilun Tibabe a kauyen Pangari na karamar hukumar Bali na jahar Taraba.
Wani mazaunin garin mai suna Pius Gura ya bayyana cewa wani bafulatani ne ya shiga gonar wani manomi dan kabilar Tibi mai suna Dooior James, tare da shanunsa, amma a lokacin da manomin ya nemi a biyashi barnar da shanun suka yi masa, sai bahillacen yasa adda ya kashe shi.
Mazaunin garin yace bayan yan uwan manomi Dooir sun samu labarin abin day faru ne sai suka tattara kansu, inda suka kai ma bahillacen harin ramuwar gayya, suka kashe shi, daga nan ne lamari ya ta’azzara.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng