Yanzu-yanzu: Shikenan, an yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

Yanzu-yanzu: Shikenan, an yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa ta hanyar rataya

Wata babbar kotun birnin tarayya Abuja dake unguwar Maitama ta yankewa Maryam Sanda hukuncin kisa kan laifin kisan mijinta Bilyaminu Bello.

Kotun ta kama Maryam da laifin kashe mijinta kuma an tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen da ake mata. Za'a ajiyeta a gidan kurkukun Suleja har ta gama daukaka kara.

Bayan Yusuf Halilu, ya kama Maryam Sanda, da laifin kashe mijinta, an yi wani gajeran rikici a cikin kotun.

Alkali Yusuf Halilu na furta cewa an kama ta da laifin kashe mijinta, Maryam Sanda ya arce daga cikin akwatin mai laifi a kotu amma ma'aikatan gidan Kurkuku da kotun suka damkota.

Rikicin ya tilastawa Alkalin tafiya hutun rabin lokaci bayan mata suka fara yi masa ihu a cikin kotun.

Yayinda daya daga cikin matan tayi kokarin zuwa wajen Maryam Sanda, Alkalin ya bada umurnin awon gaba da ita.

Yayinda muke hada wannan rahoton, Maryam Sanda na ihun “Inna lilahi Inna roji hun”, yayinda sauran yan uwanta ke kokarin bata hakuri.

Mai rahoton Daily Trust ya saurareta tana cewa: "Na yi azumi , na yi addu'a, Wayyo Allah, me yasa?

An gurfanar da ita ne kan zargin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, wanda yake dan'uwan tsohon shugaban PDP, Alhaji Bello Halliru Muhammada 2017.

An gurfanar da ita tare da dan 'uwanta, Aliyu Sanda; mahaifiyarta, Maimuna Aliyu, da mai aikin gidanta, Sadiya Aminu, wadanda ake tuhuma da kokarin boye gaskiya ta hanyar goge jinin marigayin bayan kisansa.

Bayan kammala muhawara tsakanin lauyoyi da rubuta hujjojin dukkan bangarorin biyu ranar 25 ga Nuwamba, 2019, Alkali mai shari'a, Jastis Yusuf Halilu, ya zabi yau 27 ga Junairu, domin yanke hukunci.

A ranar Laraba, 3 ga watan Yuli, 2018, kotu ta bada belin Maryam Sanda wacce ke garkame a kurkuku da laifin kisan mijinta.

Jastis Yusuf Halilu wanda ya ki bada beli a baya ya bayyana cewa akwai wani dalili kwakkwara da ya gamsar da shi kuma ya sa ya bada belin.

Alkalin ya ce rahoton asibiti ya nuna cewa Maryam na cikin wani mugun hali da jami’an fursunonin ba zasu iya kula da ita ba kuma ya gamsu ne saboda banda cewa tanada juna biyu, tana fama da ciwon Asthma.

Kwana daya kacal bayan babban kotun da ke Abuja ta bayar da belin Maryam Sanda, wadda ake tuhuma da laifin kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka har lahira ta shirya wa yar ta party na murnar zagayowar ranar haihuwa.

Taron murnar zagayowar haihuwar dai anyi shi ne ranar Alhamis, 8 ga watan Fabrairu a gidan mahaifiyar Maryam kuma ya samu hallartan yan uwan ta na jiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel