Yanzu-yanzu: EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a kotu

Yanzu-yanzu: EFCC ta gurfanar da Shehu Sani a kotu

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta gurfanar da tsohon dan majalisan dattawa da ya wakilci Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, a kotu.

An gurfanar da Shehu Sani ne da safiyar yau Litinin, 27 ga Junairu a babban kotun tarayya dake zaune a Abuja, birnin tarayya.

Ana zargin shi da laifuka biyu: Karban cin hanci da damfara.

Mun kawo muku rahoton cewa ranar 31 ga Disamba, 2019, EFCC ta damke Shehu Sani, Sanatan da ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 2015 da 2019.

An damke Shehu Sani ne kan zargin karban $20,000 daga hannun mai kamfanin motocin ASD.

KU KARANTA: Kisan Miji: Yau za'a yanke hukunci kan shari'ar Maryam Sanda

Majiyar tace: "An ce ya karbi $20,000 daga hannun mai kamfanin ASD da sunan cewa shi abokin shugaban EFCC."

"Bayan an damkeshi, ya mayar da kudin kuma an bashi beli."

"An bukaci ganinsa amma ya ba'a sameshi ba. Da alamun ya dade yana damfarar mutane da sunan shugaban EFCC."

A ranar 20 ga watan Junairu, 2020, Sanata Shehu Sani ya maka hukumar yaki da rashawa ta EFCC a kotu saboda tsaresa da tayi ba bisa ka'ida ba na kusan makonni uku.

Lauyan Shehu Sani, Abdul Ibrahim ya bayyana cewa sun mika karar gaban mai Shari'a A. B. Mohammed na babban kotun tarayya dake Gudu a Abuja.

Ibrahim ya shigar da karar ne ta bukatar bin hakkin tsohon Sanatan da EFCC da mamallakin ASD Motors. Lauyan ya bayyana cewa wanda yake karewan na bukatar naira miliyan dari ne daga hukumar yaki da rashawa ta EFCC din.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel