Boko Haram: Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 3 a Masallaci a Borno

Boko Haram: Yan kunar bakin wake sun kashe mutane 3 a Masallaci a Borno

Mutane uku sun mutu yayin da wasu 13 suka samu munanan rauni yayin da wasu mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka kai harin kunar bakin wake a wani masallaci dake karamar hukumar Gwoza na jahar Borno.

Daily Trust ta ruwaito wani sojan sa kai na Civilian JTF ne ya bayyana haka, inda yace lamarin ya faru ne yayin da Musulmai suke sallar Asubahi da safiyar Asabar, 25 ga watan Janairu a kauyen Bulabulin.

KU KARANTA: Tsohon hadimin shugaba Buhari yace Najeriya ta yi hannun riga da adalci

Jami’in Civilian JTF din ya bayyana cewa wasu mata ne yan kunar bakin wake suka yi kokarin kutsa kai cikin masallacin, amma basu kai ga shiga masallacin ba bam din ya tashi dasu. “Mata biyu yan kunar bakin wake sun shiga cikin garin Gwoza don kai hari yayin da ake Sallah.

“Amma basu samu nasara ba saboda kafin su shiga cikin masallacin bom din ya tashi, sai dai tashin bom din ya lalata masallacin gaba daya. Wani yaro dan shekara 12 ya rasu, sai kuma mutane 13 da suka samu rauni.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin ga rundunar Sojan saman Najeriya da ta yi amfani da jiragen yakinta wajen saukar da ruwan wuta a kan yan bindigan dake fakewa a dazukan jahohin Zamfara, Neja da Kaduna.

Kaakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar, inda yace shugaba Buhari ya bayyana hare hare da kashe kashen da yan bindiga suka yi a matsayin musifa ga kasa.

“Shugaba Buhari ya samu tabbacin cewa a yanzu da kurar bazara ke raguwa a sararin samaniya, jiragen yakin Soja zasu fara tashi domin kai ma yan bindiga da barayin shanu hari a yankin dajin Dogon Gona na jahar Neja.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel