Duk wanda bai samu albashi ba ya fara yajin aiki – ASUU ga Malaman jami’a

Duk wanda bai samu albashi ba ya fara yajin aiki – ASUU ga Malaman jami’a

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta umarci y’ay’anta dasu shiga yajin aiki na gama gari da zarar gwamnatin Najeriya ta dakatar da albashinsu, kamar yada wani shugaba a kungiyar ASUU ya tabbatar.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban ASUU reshen jami’ar noma na gwamnatin tarayya dake Abekuta, Dakta Adebayo Oni ne ya bayyana haka a ranar Lahadi cikin wata hirar wayar tarho da yayi da ita.

KU KARANTA: Tsohon hadimin shugaba Buhari yace Najeriya ta yi hannun riga da adalci

Oni yace uwar kungiya ta basu umarnin shiga yajin aiki nan take da zarar gwamnati ta dakatar da albashinsu. “Bisa umarnin majalisar zartawar na ASUU, ba mu bukatar gudanar da wani zaman tattaunawa.

“Umarnin shi ne da zarar an dakatar da albashinmu, zamu dabbaka dokar ‘ba biya, ba aiki’ nan take ba sai mun jira samun wani umarni daga uwar kungiya ba, saboda idan aka taba mutum daya a cikinmu tamkar an taba mu ne gaba daya.

“Da zarar an biya albashi, kuma muka gano ba’a biya wasu malaman jami’o’I ba, kai tsaye zamu shiga yajin aiki.” Inji shi.

Sai dai a hannu guda, ASUU na zargin wasu manya manyan jami’an gwamnatin Buhari da cin dunduniyar tattaunawar da gwamnati take yi dasu game da batun sabon tsarin biyan albashi na University Transparency and Accountability Solution, UTAS’

ASUU ta kirkiro da UTAS ne domin ya maye gurbin tsarin biyan albashi na bai daya, IPPIS, wanda gwamnatin tarayya ta kirkiro da shi kuma ta umarci dukkanin ma’aikatun hukumomin gwamnati su yi rajista, amma ASUU ta ki.

A jawabinsa, shugaban ASUU, Biodun Ogunyemiya bayyana cewa bai kamata gwamnati ta dakatar da albashin malaman jami’a ba saboda har yanzu akwai tattaunawa dake gudana tsakanin bangarorin biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel