'Ra'ayinka bashi da wani amfani' - Buhari ya mayar wa da TY Danjuma martani

'Ra'ayinka bashi da wani amfani' - Buhari ya mayar wa da TY Danjuma martani

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ra'ayin Theophilus Danjuma ba shi da amfani fiye da na miliyoyin 'yan Najeriyan da suka kada masa kuri'a don tabbatar da zarcewarsa a 2019.

Buhari ya yi wannan tsokacin ne a tattaunawar da shugaban kasar yayi da The Interview ta yanar gizo kuma aka saki a Abuja a ranar Asabar.

Wata takardar da aka bai wa manema labarai wacce ta fito daga hannun babban editan tattaunawar a ranar Lahadi, ta bayyana manyan tsokacin da shugaban kasar yayi.

Da aka tambayi Buhari a kan kuri'ar rashin kwarin guiwa wacce Danjuma ya bayyana a sabon littafinsa, ya ce: "Wannan ra'ayinsa ne kuma bai dameni ba. Kuri'ar kwarin guiwar da 'yan Najeriya suka kada min a zaben 2019 ce ta fi min komai ba ra'ayin mutum daya ba."

Idan zamu tuna, Danjuma ya ce da 'yan Najeriya sun san abinda ke faruwa a gwamnati, da basu dinga bacci ba.

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi: Dattijan APC a Kano sun juya wa Kofa baya, dan takarar PDP na kan hanyar lashe zabe

Wannan tsokacin kuwa ya jawo cece-kuce ba kadan ba kuma ya nuna rashin kwarin guiwa a kan gwamnatin nan daga mutumin da ake kallo a matsayin wani jigo ga Buhari.

Amma kuma shugaban kasar ya ce kara zabensa da 'yan Najeriya suka yi na nuna kwarin guiwa tare da goyon bayan shi da gwamnatin shi da 'yan Najeriya ke yi.

A kan dangantakarsa da mataimakinsa Yemi Osinbajo, Buhari ya ce komai 'zam-zam' ya ke tsakaninsu. Da aka bukaci shugaban kasar ya bayyana yanayin dangantakarsa da mataimakinsa a kan sikelin daya zuwa 10, sai yace "komai dai-dai. Ko yayi korafi ne?"

Ya kara da tsokaci a kan yadda ake yada cewa 'miyagu' ke rike da mulkin kasa sannan alkawarinsa na dage 'yan ajeriya miliyan 100 daga talauci duk na bogi ne, ya ce wannan zance ne mara tushe ne balle makama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel