Shugaba Buhari ya yabawa Matawalle kan yadda ya magance matsalan tsaro a jihar Zamfara

Shugaba Buhari ya yabawa Matawalle kan yadda ya magance matsalan tsaro a jihar Zamfara

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Asabar ya yabawa matakin da gwamna Bello Matawalle ya dauka wajen dakile yan bindiga, masu garkuwa da mutane da yan barandan a jihar Zamfara.

Shugaban kasan ya bayyana yabonsa ne a jawabinsa na taron yaye daliban jami'an tarayya dake Gusau, babbar birnin jihar Zamfara.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa rikicin da ya kwashe kimanin shekaru goma a jihar ya fara sauki bisa ga shirin sulhu da gwamnan ya samar.

Buhari ya ce wannan shiri ta haifar da 'da mai dio wajen ceto wadanda akayi garkuwa da su tare da amsan makaman yan bindiga.

Shugaban kasa ya bayyana cewa lallai za'a kawo karshen matsalar tsaron da ake fama dashi kuma yayi kira sauran jihohi su bi sahun jihar Zamfara.

DUBA NAN: Zaben kujerar majalisan wakilai: Dan takaran PDP ya doke APC a Bauchi

A wani labarin daban, Jam'iyyar All Progressives Congress APC shiyar jihar Zamfara ta yabawa gwamnatin abokin hamayyarta, Mohammad Bello Matawalle, kan soke dokar baiwa tsaffin gwamnoni, mataimakansu, tsaffin kakakin majalisa da mataimakansu makudan kudi da sunan alawus.

Jam'iyyar ta laburta wannan ne ta bakin mataimakin shugaban yankin Zamfara ta tsakiya, Sani Gwamna.

Gwamna wanda yayi hira da manema labarai bayan ganawar jigogin jam'iyyar a Gusau, ya bukaci gwamnatin tayi amfani da kudaden wajen ayyukan jin dadin al'ummar jihar.

Kan lamarin tsaron jihar kuwa, Sani Gwamna ya bayyana cewa wasu yan siyasa na amfani da yan bindigan wajen cimma manufarsu ta siyasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel