2023: Buhari bai yi alkawarin mika wa Tinubu mulki ba - Shugaban NIWA

2023: Buhari bai yi alkawarin mika wa Tinubu mulki ba - Shugaban NIWA

Tsohon sakatare jam'iyyar All Progressives Congress and Chairman na kasa kuma shugaban Hukumar kula da hanyoyin ruwa na cikin gida wato NIWA, Goerge Muoghalu ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi alkawarin zai mika wa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu mulki ba.

Muoghalu, yayin zantawa da ya yi da manema labarai a jihar Imo a ranar Asabar, ya ce akwai yiwuwar dan kabilar Ibo ya maye gurbin Shugaba Buhari kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sai dai ya ce akwai bukatar jam'iyyar mai mulki da kara samun karbuwa a jihohin Kudu maso gabashin kasar.

Muoghalu ya ce shugaban kasar ya yi wa mutanen Kudu maso gabashin kasar adalci.

2023: Buhari bai yi alkawarin mika wa Tinubu mulki ba - Shugaban NIWA
2023: Buhari bai yi alkawarin mika wa Tinubu mulki ba - Shugaban NIWA
Asali: Facebook

Ya kuma ce duk da hakan akwai bukatar Shugaba Buhari ya kara gwangwajewa mutanen yankin romon demokradiyya domin hakan yasa suke zarginsa da mayar da su saniyar ware.

Tsohon sakataren APC na kasa ya ce jam'iyyar mai mulki za ta iya lashe zaben gwamna a jihar Anambra a 2021 muddin ta fitar da dan takara mai nagarta da mutane za suyi na'am da shi.

DUBA WANNAN: An sake kashe kwamandan kasar Iran

Shugaban na NIWA ya ce tunda APC ta karbe jihar Imo, hakan ya nuna tana samu karbuwa wurin talakawa na yankin Kudu maso gabas.

Ya ce ya gamsu da yadda jam'iyyar ta yi sulhu tsakanin 'ya'yanta sakamakon rikicin cikin gida da ya barke a APC reshen jihar ta Imo.

"Wane ya fada muku cewa Buhari ya yi alkawarin zai mika wa Tinubu mulki. Babu wani yarjejeniya mai kama da hakan saboda haka mutane su dena yada maganganun da ba su da tushe.

"Ina kyautata tsamanin cewa APC za ta iya lashe zaben shugaban kasa a 2023 amma akwai bukatar mu kara kafa gwamnati a wasu jihohi. Idan mun tsayar da dan takara na gari, APC za ta lashe Anambra. Shugaban kasa ya yi ayyuka masu kyau a Kudu maso gabas amma duk da haka mutanen na bukatar kadi," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel