Barazana ga iyaye kan kin kai yaransu makaranta: Iyaye sun mayarwa El-Rufa'i martani

Barazana ga iyaye kan kin kai yaransu makaranta: Iyaye sun mayarwa El-Rufa'i martani

A ranar Juma'a, gwamnatin jihar Kaduna ta yi kira ga iyaye su tura yaransu makaranta ko su fuskanci fushin hukumar bisa da dokokin da jihar ta ayyana.

Sakatariyar din-din-din ta ma'aikatar Ilimin jihar, Phoebe Yayi, ta yi wannan kira ne a hirar da tayi da kamfanin dillancin labarai a Kaduna.

Madam Phoebe tace hakkin ko wani yaro ne ya samu ingantaccen ilimin firamare kuma kyauta, saboda haka wajibin gwamnatin jihar ne ta samar da hakan.

Ta ce saboda wajabcin haka aka alanta Ilimi kyauta da dukkan yaran jihar Kaduna daga Firamare zuwa Sakandare a jihar.

Martani kan wannan barazanar, tsohon sakataren ilimin karamar hukumar Kaduna ta kudu, Sanusi Sirajo, ya bayyanawa manema labarai cewa hukunta iyayen ba shi bane mafita.

Ya ce abinda ya kamata gwamnati tayi shine wayar da kan iyaye tare da fadakar da su kan muhimmancin tura yaransu makaranta ta hanyar amfani da sarakunan gargajiya.

Surajo ya ce wayar da kan iyaye kan muhimmancin ilimin yaransu ne mafita.

Wani masanin harkar Ilimi a Tudun Wada, Abdulganeeyu Abdurrahman Giwa, ya yi kira ga gwamnan ya jawo hankalin da iyayen kafin yi musu barazana.

"Kamata yayi a jawo hankalin iyayen kafin yi musu barazana. Akwai bukatar a sanar da iyayen amfanin da zasu girba idan suka bari yaransu suka shiga makaranta saboda a yanzu, akwai iyayen da ke ganin zuwa makarantar yara bai da amfani." Yace

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel