Zaben maye gurbi a Kaduna: Jama'a sun kaurace wa wuraren kada kuri'a

Zaben maye gurbi a Kaduna: Jama'a sun kaurace wa wuraren kada kuri'a

Zaben maye gurbi na majalisar jihar Kaduna da ake yi a karamar hukumar Sanga ta jihar ya samu rashin fitowar masu kada kuri'u. Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta saka yau Asabar ne don yin zaben maye gurbin na kananan hukumomin Sanga da Kagarko na jihar Kaduna.

Shugaban karamar hukumar Sanga, Charles Danladi, ya ce ba abin mamaki bane don masu kada kuri'a basu fito kadawa ba saboda an fi mayar da hanklai wajen zaben duka garin.

"Mutane da basu fito kada kuri'un ba sune wadanda suka yi rijista a nan amma ba a nan suke zama ba. Mutane da yawa basu iya doguwar tafiya don zuwa kada kuri'u saboda ba zaben duka gari bane," cewar Danladi.

Danladi wanda ya nuna gamsuwarsa da yadda zaben ke tafiya da yanayin jami'an tsaro, ya yi kira ga jama'a da su kiyaye zaman lafiyar da ke wanzuwa a yayin zaben.

Zaben maye gurbi a Kaduna: Jama'a sun kaurace wa wuraren kada kuri'a
Zaben maye gurbi a Kaduna: Jama'a sun kaurace wa wuraren kada kuri'a
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi a Sokoto: Jama'a sun yi tururuwar fito wa domin kada kuri'a

Hakazalika, Emmanuel Jakada, shugaban jam'iyyar APC na jihar ya ce ya ji dadin yadda zaben maye gurbin ke gudana. Ya jinjinawa masu kada kuri'u ta yadda suke komai cikin lumana.

Jakada ya musanta zargin da ake wa APC na tura 'yan daba don tada zaune tsaye wajen zaben. Zaben maye gurbin na karamar hukumar Sanga za a yi shi ne a gundumomi 14 na karamar hukumar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel