Ikon Allah: Mamaki ya rufe mutane yayin da suka ga katon hannu ya bayyana a sararin samaniya

Ikon Allah: Mamaki ya rufe mutane yayin da suka ga katon hannu ya bayyana a sararin samaniya

- Wani abin mamaki da al'ajabi ya faru a biranen Asuncion da Juazeirinho a kasar Brazil

- Jama'ar biranen sun ga wasu hannaye sun bayyana a sararin samaniya wadanda suka kira da 'hannayen Ubangiji'

- Wasu daga cikin mazauna yankunan sun dinga kiran hakan da mu'ujiza amma wasu na ganin tamkar wani mummunan lamari ne zai auku

Mutane sun ga wani abu wanda suka kwatanta da hannayen ubangiji a biranen Asuncion da Juazeirinho da ke yankin Paraiba Cariri da ke kasar Brazil.

Mazauna yankin sun dauka hotunan sararin samaniyar kafin hannayen su rabe.

Mazauna yankin sun dinga wallafa hotunan a kafafen sada zumuntar zamani. Daya daga cikin mazauna yankin ya ce "kalli wannan kyawawan hannayen, a koda yaushe hannayen ubangiji na jiran bawan shi."

Abin mamakin kuwa shi ne yadda sararin samaniyar yankin a Brazil yake tangaran babu hadari.

Mutane da yawa sun ji dadin wannan mu'ujizar da suka gani a sararin samaniya. Wasu mutane kuwa sun yi tunanin wannan wata alama ce ta girman Ubangiji.

"Ina fatan wadannan hannayen ba wata alama ba ce ta abin alhini ko yaki", daya daga cikin mazauna yankin Asuncion ya wallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel