Ko me yayi zafi haka: Saurayi yayi tafiyar kilomita 300 domin ya kashe budurwar shi

Ko me yayi zafi haka: Saurayi yayi tafiyar kilomita 300 domin ya kashe budurwar shi

- Rundunar 'yan sandan yankin Kinangap da ke Nyandarua a kasar Kenya sun kama wani mutum mai shekaru 25

- An zargi mutumin da yin tafiyar kilomita 300 don halaka tsohuwar masoyiyar shi har lahira

- Ya isa gidanta da yammaci inda ya samu wuka ya sossoketa a bangarorin jikinta wanda hakan ya kawo sanadin mutuwarta

Rundunar 'yan sandan yankin Kinangop da ke Nyandarua a kasar Kenya sun kama wani mutum mai shekaru 25 wanda ake zargi da kashe wata mata mai shekaru 22.

Wanda ake zargin mai suna Allan Musila na aiki ne a matsayin mai gadi da G4S a yankin Kakamega. Ya isa gidan marigayiyar ne da ke yankin Weru a Kinangop da yammacin ranar Talata, 21 ga watan Janairu, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Bayan hayaniyar da ta fara tashi tsakaninsu, sai mutuwarta ta biyo baya.

'Yan sanda sun ce Musila ya soki masoyiyar shi Consolata Wambui, malama a babbar makarantar St. Michael a Nyandarua, sau ba adadi da wuka.

Wambui ta samu raunika masu yawa a kanta da kirjinta. Dan uwan Wambui wanda ke zama kusa da ita ya sanar da manema labarai cewa ya ji ihunta tana neman taimako kuma koda ya isa inda ta ke, ya tarar da Musila rike da wuka jini na zuba.

KU KARANTA: Ba a wannan lokacin ya kamata shugaba Buhari yayi mulki ba - Kashim Shettima

Dan uwanta din ya ce yayi kururuwar da ta jawo hankalin makwabta wadanda suka hanzarta kaita asibiti bayan sun kwace wukar hannun wanda ake zargin.

An kira 'yan sanda zuwa inda abin ya faru kuma sun kama wanda ake zargin.

Wambui ta rasu a daren ranar Talata a asibiti sakamakon raunikan da ta ji. An ajiye gawarta a ma'adanar gawawwaki da ke asibitin yankin. Likitoci sun ce Wambui ta rasa jini mai tarin yawa ne kuma hakan ya jawo mutuwar ta.

'Yan uwan Wambui sun ce Musila tsohon masoyin 'yar uwarsu ne kuma sun sha mamaki da suka samu labarin yadda masoyinta ya yi tafiyar kilomita 300 don halakata.

Rahoto ya nuna cewa suna da diya tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel