An sake kashe kwamandan kasar Iran

An sake kashe kwamandan kasar Iran

Wasu yan bindiga sun kashe wani kwamandan dakarun Basij na kasar Iran Abdolhossein Mojaddami a birnin Darkhovin a ranar Talata a kofar gidansa kamar yadda kamfanin dillancin labarai na IRNA ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne makonni bayan kisar da Amurka ta yi wa tsohon kwamandan sojojin Iran Qassem Soleimani a kasar Iraqi ta hanyar amfani da jirgi mara matuki. Yan bindigan sun taho kan babura ne inda suka bude masa wuta sannan suka tsere ba tare ta an gano ko su wanene ba.

Mojaddami shine ke jagorancin dakarun Basij, wadda wani bangare ne na sojojin kasar da ke kula da tsaron cikin gida da wasu ayyuka musamman a Darkhoein da kudu maso yammacin Iran.

Rahotanni sun ce yana da kyakyawan alaka da Soleimani, tsohon shugaban dakarun Iran da Amurka ta kashe a ranar 3 ga watan Janairu.

Wannan na zuwa ne bayan kasar Amurka ta gindaya wa Iran sabbin takunkumi sakamakon kisar da dakarun sojojin kasar suka yi wa mutane masu zanga-zanga fiye da dari a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

DUBA WANNAN: An damke wani namiji da ya yi shigan mata don a dauke shi aikin kula da gida

Amurka ta ce ta dauki matakin ne sakamakon rahotanni da aka wallafa a kafafen yadda labarai da kuma korafe korafe da mutanen Iran suka yi ta hanyar amfani da wani tsari na musamman na tabbatar da adalci a kasar.

Majiyar ta yi ikirarin cewa dakarun na kasar Iran sun kashe a kalla masu zanga zanga 148 ta bindiga da kuma bankawa wani kududufi wuta da masu zanga-zangan suka shiga don tsira da rayyukansu.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya ko kasa da ta fito ta dauki nauyin kissan kwamandan sai dai wasu masu nazarin alamura na zargin akwai hannun Amurka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164