Tashin hankali: Wani mutumi ya ciji kare ya mutu murus

Tashin hankali: Wani mutumi ya ciji kare ya mutu murus

- Abin mamaki ba ya taba karewa a duniya don wasu labaran kama suke da almara

- Wani Kare ne ya mutu bayan wani mutum mai 'dafi' ya rama cizon da ya yi mishi

- Kamar yadda kanin mutumin yayi bayani, Karen ya mutu ne cikin kuna bayan cizon tare da kumfa da ke bayyana guba ce ta kashe shi

Bayan tsohon shugaban kasa Mahama ya wallafa wani bidiyo wanda aka ga bera na fatattakar katuwar mage kuma mutane na fassara shi daban, sai ga bullowar wani lamari makamancin hakan a yankin Volta na kasar ya faru.

Bidiyon ya nuna yadda wani kare ke mutuwa ne bayan wani mutum mai 'dafi' ya cije shi.

Lamarin ya faru ne a wani yanki da ake kira Adafienu kusa da Denu a yankin Volta na kasar Ghana.

Kamar yadda rahoton gidan talabijin din UTV da ke yankin Volta ya nuna, mutumin mai suna Jastis Aflakpui wanda aka fi sani da Efo na hutawa ne yayin da Karen ya tinkare shi ya cije shi.

Kamar yadda dan uwan shi ya sanar da gidan talabijin din UTV, Efo ya fusata ne kuma ya bi Karen tare da kama shi kuma ya rama cizon da yayi mishi wanda hakan ya jawo mutuwar Karen kusan a take.

KU KARANTA: Za a kafa dokar tilastawa masu yiwa mata fyade su dinga aurensu

Ya kara da cewa, bayan cizon Karen, ya fadi yana kuka cike da tausayi kafin daga baya ya mutu.

"Ya ji matukar zafin cizon Karen. Cikin fushi ya bi shi har zuwa wani daji da ke kusa inda ya rama cizon. Ya yi sa'ar shake Karen tare da manna mishi cizon ramuwa. Na ji labarin yadda Karen ya dinga kuka sannan ya mutu cikin mintoci kadan. Na je dubawa amma sai na tarar Karen ya mutu da kumfa a bakin shi," dan uwan Efo ya sanar wa manema labarai.

Tirkashi! Abin mamaki ba ya karewa a duniya kuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel