Sai ka yi nadama bayan mulkinka - Kwankwaso ya yiwa Ganduje raddi

Sai ka yi nadama bayan mulkinka - Kwankwaso ya yiwa Ganduje raddi

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanata, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa tsoron abokin tafiyarsa, gwamna Abdullahi Umar Ganduje, da mabiyansa ba tantama za suyi nadama bayan karewar wa'adinsa matsayin gwamna.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani hira da ya gabatar da gidajen rediyon jihar Kano.

A cewarsa, gwamnatin jihar Kano a yau na jagorantar al'umma ne bisa ga yaudara da karerayi kuma hakan zai sa gwamnan yayi nadama a karshen wa'adinsa.

"Ko shakka babu za suyi nadama a karshen milkinsu, za suyi da sun sani sun mikawa wanda ya lashe zaben 2019 mulki," Kwankwaso yace.

Mun kawo muku rahoton cewa Mai magana da yawun tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran mazhabar Kwankwasiyya, Hajiya Binta Spikin, ta sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Hajiya Sipikin ta sanar da sauya shekarta ne ranar Laraba, daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Wanna ya biyo bayan sauya shekan shugaban jam'iyyar PDP na jihar Kano, Rabiu Sulaiman Bichi, daga PDP zuwa APC.

A jiya, Ganduje ya bayyana cewa Kwankwaso na shirya komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC) domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa a 2023.

Ya bayyana hakan ne yayinda ya karba shugaban jam'iyyar PDP na darikar Kwankwasiyya na jihar Kano, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

A yayin ziyarar da suka kai gidan gwamnatin jihar, Gwamna Ganduje ya karbesa tare da sauran shugabannin Kwankwasiyya na kananan hukumomi 44 na jihar.

Yayin bikin karbar Bichi tare da sauran jahororin Kwankwasiyya na kananan hukumomin Kano 44, Ganduje ya fada musu cewa "wannan jar hula bata dace daku ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel