Yanzu-yanzu: An tabbatar da bullar cutar Lassa a Bauchi

Yanzu-yanzu: An tabbatar da bullar cutar Lassa a Bauchi

Cibiyar Lafiya Bai Daya na jihar Bauchi ta tabbatar da bullar cutar zazzabin Lassa a jihar a shekarar 2020.

Babban sakataren cibiyar, Dr. Rilwanu Mohammed, ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a a Bauchi yayin da ya ke yi wa manema labarai bayani, ya ce har yanzu dai babu wanda ya mutu cikin wadanda suka kamu da cutar.

Ya ce an aike samfuri samfuri daga wasu mutane 15 zuwa Cibiyar Kulawa da Cututtuka ta Abuja da ke zargin zazzabin Lassa ne domin a tabbatar ko cutar ne kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mohammed ya ce zazzabin na Lassa ba sabon abu bane a jihar inda ya ce jihar tana daga cikin jihohin da cutar ya saba bulla.

DUBA WANNAN: Rashawa: Ba zan sassauta wa Abubakar ba - Gwamnan Bauchi

Ya ce, "Mun samu labarin rasuwar wasu a Kano sakamakon zazzabin Lassa kuma ana zargin bullar cutar a Bauchi. Wannan shekarar a Bauchi, mun samu mutane 15 da ake zargin suna dauke da cutar ta Lassa, an tabbatar da uku cikinsu yayin da wasu 12 kuma da ake zargin ba cutan bane.

"Abinda ya faru shine akwai wata mata da ke zaune a Kano ta zo Bauchi don ziyarar 'yan uwanta kuma ta yi wasu kwanaki a Bauchi sannan daga baya ta tafi wani kauye a karamar hukumar Toro. An fi tsamanin samun cutar ta Lassa a Toro, Bauchi da Tafawa Balewa.

"Ta tafi can kuma a can ne cutar da bulla amma bana so in ce komai a kai domin a matsayi na na kwararre mai nazarin yaduwar cutar, bana son inyi magana kan abinda bai faru a nan Bauchi ba. Amma dai tun farko cutar a karamar hukumar Toro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel