Duk macen da bata son kudi ba macen aure ba ce - Reno Omokri

Duk macen da bata son kudi ba macen aure ba ce - Reno Omokri

- Marubuci kuma lauya Reno Omokri ya sanar da maza cewa duk macen da bata son kudi bata cika mace ba

- Tsohon hadimin shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayin sukar mazan da ke caccakar mata masu son kudi

- Mutane na cewa son kudi ne tushen fitina amma Reno Omokri ya ce kin kudi shine tushen fatara da talauci

Marubuci kuma lauya, Reno Omokri ya sanar da maza cewa duk macen da bata son kudi ba 'kadara' ba ce.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya sanar da hakan ne yayin da yake mayar da martani ga mazan da ke tsanar mata masu son kudi, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.

A kalaman shi; "Ina matukar mamakin yadda wasu mazan ke caccaka tare da sukar mata masu son kudi. Babu wani littafin addini da ya ce kada a so kudi. 'Son kudi shi ne tushen sharri'. Amma kuma rashin son kudi a wajena zan iya cewa shi ne tushen talauci da fatara. Duk macen da ba ta son kudi ba kadara ba ce."

KU KARANTA: Tirkashi: Saurayi ya mutu a yayin da yayi tsalle domin ya kamo wayarshi ta dubu 3 da ta fada rijiya

Akwai bukatar dan Adam; mace ko namiji su so kudi don hakan ne kadai zai sa a jajirce a nemi kudin. Rashin son kudin na sa mutuwar zuciya tare da lalaci mai tarin yawa ga matan ko mazan.

Abinda jama'a ke soka shi ne yadda wasu matan ke son kudi ba tare da sun nema ba. Burinsu su samu samari ko miji mai kudi wanda zasu ci a sama ba tare da sun wahala ba. Hakan kuwa babban rashin dabara ne kuma yana matukar haifar da mutuwar zuciya.

Ga wasu kuwa, a rashin sa'a suke fada wa hannu da ba na gari ba wanda hakan ke haifar musu da matukar dana-sani har karshen rayuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel